ABIN DA ALKUR'ANI YA KE CEWA AKAN YAKI

A Alkur’ani, yaki ya kasance “aikin dole” da ake yinsa a bisa dole wanda kuma ake aiwatar da shi da taka-tsantsam bisa ka’idoji da kiyaye hakkin dan Adam, wanda kuma sai ya zama tilas ake yinsa.

A cikin wata aya ta Alkur’ani, an bayyana cewa kafirai ne masu neman tada fitinar yaki kuma Allah ba ya son tada fitina:

… ko da yaushe suka hura wata wuta domin yaki, sai Allah ya bice ta. Suna aikin a cikin kasa domin barna, alhali kuwa Allah ba Ya son masu fasadi. (Alkur'ani, sura ta 5, aya ta 64)

Ta fuskar yaki, ba a shiga har sai in ya zama ba makawa dole sai an yi. An baiwa masu imani umarnin gwabza yaki ne yayin da abokan gaba suka far musu sannan kuma cewa babu wata hanyar kare kai daban in ba yakin ba:

Sa'annan idan sun hanu, to Allah Mai gafara ne, Mai jin kai. (Alkur'ani, sura ta 2, aya ta 192)

öldürmek, cinayt
Hoton Madinah a yau, birnin da Annabi Muhammad (SAW) da al'ummar Musulmi suka yi hijira zuwa cikinsa inda suka kafa gwamnatinsu.

Kyakkyawan nazari kan rayuwar Annabi Muhammad (SAW) zai nuna mana cewa ana gwabza yaki ne a matsayin matakin tsaro, shi ma in ya zama dole.

Annabi (SAW) ya karbi wahayi har tsawon shekaru 23. Cikin shekaru 13 na farkon kiransa, musulmai a lokacin ‘yan kadan ne kuma sun zauna karkashin mulkin maguzanci na jahiliyya a Makka inda suka dandana bakar wahala. Da damansu sun fuskanci tsangwama, cin mutunci da azabtarwa iri iri, har ma da kisa, aka kwace gidaje da dukiyoyinsu. Amma duk da wannan tsangwama, haka musulmin suka daure da hakuri ba tare da sun dauki hanyar tashin hankali ba, kuma a haka suka ci gaba da isar da sako ga mutanen Makka.

Yayin da zaluncin mutanen Makka ya kai makura, sai musulmai suka yi hijira zuwa garin Yathrib, wanda daga bisani ya zama Madina, inda za su sami ‘yancin gudanar da addininsu ba tare da fuskantar tsangwama ba. Hatta bayan sun kafa gwamnatin musulunci hakan bai sa sun kaiwa maguzawan Makka farmakin ramuwar gayya ba. Sai bayan saukar da wannan ayar ne Manzo (SAW) ya umarci jama’arsa da su yi shirin yaki:

An yi izini ga wadanda ake yakarsu da cewa lalle an zalunce su, kuma hakika Allah Mai ikon yi ne a kan taimakonsu. Wadanda aka fitar daga gidajensu ba da wani hakki ba face suna cewa "Ubangijinmu Allah ne."… (Alkur'ani, sura ta 22, aya ta 39-40)

A takaice, an baiwa musulmai damar yaki ne sakamakon zalunci da kisan da ake yi musu. A sassaukan bayani, Allah Ya bayar da umarnin yaki ne don kare kai kawai. A cikin wasu ayoyin, an gargadi musulmai akan shisshigi da ketare iyaka akan abokan gabarsu:

Kuma ku yaki wadanda suke yakarku, a cikin hanyar Allah, kuma kada ku yi tsokana, lalle Allah ba Ya son masu tsokana. (Alkur'ani, sura ta 2, aya ta 190)

Bayan saukar wadannan ayoyi, an gwabza yakukuwa tsakanin musulmai da kuma maguzawan Larabawa. Kuma duk a cikin yakukuwan babu wanda musulmai ne suka fara kai hari a cikinsa. Bugu da kari, Ma’aiki Muhammad (SAW) ya shimfida tsari wanda ya wanzar da yanayin tsaro da aminci ga musulmai da maguzawan baki daya ta hanyar yarjejeniyar Hudaibiyya wadda a zahiri ma ta fi anfanar maguzawan. Har ila yau dai, su maguzawan su ne suka fara saba yarjejeniyar suka yaki musulmai. A sakamakon musulunta da yawan mutane suke yi, sai yawan sojojin musulmai ya karu inda suka gagari rundunonin maguzawan. Amma duk da wannan, Manzan Allah (SAW) ya bude birnin Makka ba tare da zubar da jinni ba saboda jin kai irin nasa. Haka kuma Ma’aiki bai nemi daukar fansa akan shugabannin Makka ba bayan ya bude garin. Bai cutar da kowa ba, hasali ma afuwa ya yi musu tare da karramawa. Da yawansu sun yi mamakin irin wannan hali na Manzon Allah (SAW), wanda sanadin hakan suka rika karbar musulunci don radin kansu.

-(SAW), an tsare hakkin raunana da marasa karfi. A lokuta da dama Ma’aiki (SAW) ya sha fadakar da masu imani akan wannan al’amari inda kuma a aikace ya kasance jagora abin koyi ga al’umma. Hakika, ga yadda ya fadakar da masu imani yayin da suke shirin fita zuwa yaki: “Ku fita yaki don amsa kiran addinin Allah. Kada ku taba tsofaffi, mata da yara. Ku kasance masu kyautatawa tare da tausaya musu. Allah yana son masu ikhlasi.” Haka nan Manzon Allah ya yi bayanin irin halayyar da musulmai za su dauka koda kuwa suna tsakiyar filin daga ne:

Kada ku kashe kananan yara. Ku guji taba mutanen da suka kebance kansu cikin bauta coci coci! Kada ku kasha mata da tsofaffi. Kada ku kone ko sare bishiyoyi. Kada ku rushe gidaje!3

mekke, kutsal şehir

Tsarin dabi’ar addinin musulunci wanda Allah ya saukar a cikin Alkur’ani shine asalin wannan tsarin mai sassauci da lumana na Annabi Muhammad (SAW). A cikin Alkur’ani, Allah yana umartar musulmai da su kasance masu kyautatawa da kuma yin adalci ga wadanda ba musulmai ba:

Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayin daka domin Allah, masu shaida da adalci. Kuma kada kiyayya da wasu mutane ta dauke ku akan ba za ku yi adalci ba. Ku yi adalci. Shine ma fi kusa ga takawa. Kuma ku bi Allah da takawa. Lalle Masani ne da abin da ku ke aikatawa. (Alkur'ani, sura ta 5, aya ta 8)

kabe, mekke

Ka'aba, inda kusan Musulmai miliyan biyu suke zuwa kowace shekara daga kusurwowin duniya hudu don yin ibada, alama ce ta zaman lafiya da tausayi wadanda bangare ne na koyarwar musulunci.

Cikakkiyar Ma'anar Jihadi a Alkur'ani

A jihadi na cikin Alkur’ani babu kashe kashe. A jihadi na Alkur’ani babu ruwan bamabamai. Babu ‘yan kunar-bakin-wake ko hare haren sari-ka-noke akan mutanen da ba ruwansu.Babu kiyayya ko la’antar mutane a cikin jihadi na Alkur’ani. A jihadin cikin Alkur’ani ba a tsine wa ‘ya’yan Annabi Ibrahim (AS), na Annabi Yaqub (AS) da kuma Annabi Musa (AS). Babu barazana da tursasawa a jihadi na Alkur’ani. Musulunci ba addinin shaci-fadi da hauma hauma ba ne. Babu batun yanka, mutuwa, kiyayya da mugun fushi a musulunci, haka ma a Kiristanci da Yahudanci.

Saboda haka, idan wani zai zo ya ce “Alkur’ani ne ya ce in kashe mutane, fasa bam da la’antar mutane” to karya yake yi, ko kuma an wanke kwakwalwarsa ne. Dan ga-ni-kashe-ni ne kawai wanda ke ikrarin musulunci amma yake bin addinin da aka kirkira da manufar kisa, fasa bamabamai da kuma la’antar mutane. Babu abin da ya hada asalin wannan kirkirarren addini da Alkur’ani. Ba lalle ba ne sun fahimci abin da ke cikin Alkur’anin da suke sumbanta suna dora shi a goshinsu ko su rataye shi a bango.

Wannan shi ne bakin addini wanda komai na cikinsa baki ne. Yana yada kiyayya maimakon son juna, fushi maimakonnuna kauna, kiyayya maimakon 'yan uwantaka, bala'I maimakon kyawun dabi'a da kuma jahilci maimakon ilimin fasaha, kimiyya da na al'adu. Abu ne mai sauka a damka bindiga a hannun wanda ke bin irin wannan addinin. Abu ne mai sauki a ce, "Wadancan mutanen makiyanka ne." Abu ne mai sauki a tunzura irin wadannan mutane. Samar da fitinannun al'ummu ba abu ne mai wuya ba. Wannan muguwar annoba, wadda ba a cikin musulunci kadai ake samunta ba har ma a duk sauran addinai hatta Markisanci, addinin bautar shaidan da kuma zahiranci. A takaice a dukkan addinai, akidu da hanyoyin tunani, akan sami annobar ra'ayin ga-ni-kashe-ni.

Me yake haifar da tsattsauran ra'ayi? Saboda shine abin da ake koyawa mafi yawan mutane. Ba su san wani addini ba sai wannan. Wannan shine kadai abin da 'yan ga-ni-kashe-nin da suke kiran kansu musulmi suka sani. An barsu cikin duhun kai da jahilci. An nisanta su da al'umma, sun guji ilimin fasaha da na kimiyya. Dama ba su san ainihin jihadi ba don haka suke yin aika aika da sunan jihadin tun da haka aka koya musu. Koda yaushe tunaninsu shine su aikata abin da ake koya musu don samun lada da daukaka. Ba su taba tunanin cewa suna cutar da kansu, addini, iyali da kuma sauran jama'a suke cutarwa ba.

Sai dai kuma yadda jihadi yake a Alkur'ani ya sha bamban da yadda suke tsammani. Kalmar jihadi ta samo asali ne daga kalmar larabci ta – "jahd." Ma'anarta shine: 1. Yin aiki, kokari, sadaukarwa, yunkuri. 2. Tsare sha'awar mutum. A musulunci, yana nufin a sanar da daya bangaren, a koyar da kyakkyawar dabi'a, da yin kokari don kauda mutane daga mummunan aiki da nuna so da tausayawa. Ma'ana dai, abin da ya kamata musulmin da yake yin "jahd" ya yi shine ya yi kokarin yada soyayya, aminci da kaunar juna sannan ya koyar da mutane abin da zai kautar da su daga aikata mummunan aiki. Jihadi musulmi na biyu shine yaki da zuciyarsa. Hakan ya hada da zama mutumin kirki ta hanyar juya baya ga munanan ayyuka, kiyayya da fushi tare da rike sha'awarsa.

Masu tsattsauran ra'ayi ba su san wannan ba. Saboda haka, zagi, la'anta, barazana, kullewa a kurkuku ko korar mutumin da yake ganin kashe kashen da yake yi jihadi ne ba shi da wani amfani. Wannan mummunar fahimta da take cikin kwakwalwarsa ba za a iya fitar da ita da makami ko azabtarwa ba. Koda an kashe shi, ba za a iya kashe ra'ayinsa ba. Wannan baudadden ra'ayi zai ci gaba da haifar da baudaddun mutane. Za ka iya dushe tasirin akida ne da wata akidar. Babu wata hanya banda wannan. Matsalar ita ce rashin ilimi. Kuma don a iya ilmantar da wannan mutum, kana bukatar malamai wadanda koda yaushe za su rika yada gaskiya, son juna da zaman lafiya tsakanin mutane. Akwai bukatar mutane suka karkakata ga aiwatar da sabuwar hanya wadda ba a taba gwada ta ba. Suna bukatar su fara magana da sabon yare, wato "yaren aminci."

Abu ne mai sauki ka ji ana tsinewa mutane yayin da rai ya baci. Amma harshen aminci da lumana yana da bambanci. Babu "'yan ta'adda" a harshen zaman lafiya, sai dai jahilai, da masu karancin ilimi. Wannan yana da muhimmanci, saboda abu ne mai wuya mutum ya saurari wa'azinka yayin da ka kira shi da dan ta'adda; kana kiran sa da haka yana kara maida kansa dan ta'addar. Babu rushe rushe ko nuna karfi a harshen aminci, koda kuwa akwai abubuwan da suka kawo fushi da kiyayya. Babu mutane da saboda fusata za su ce, "Kai maci-amana ne, dan ta'adda" a harshen aminci, sai dai malamai da za su rika cewa "Akwai kuskuren fahimta cikin ra'ayinka." Muna da bukatar mutane na musamman, gungun mutane na musamman wadanda suka yi watsi da harshen fushi wanda ake amfani da shi shekaru aru aru wanda ba abin da ya kara ban da kiyayya da kashe kashe, wadanda kuma a maimakon sa suka dauki harshen aminci, wanda ke bukatar hikima, sadaukarwa da kyawawan dabi'u. Maimakon shiga cikin rundunar 'yan tsinuwa, wadanda ba su taba warware wata matsala ba, ya kamata mu nemo hanyoyin warware wadannan bakaken al'amura a matsayinmu na mutane masu madaukakiyar fahimta da ke yin amfani da harshen aminci.

Babu wata kasa ko al'umma da ta taba gwada wannan hanya saboda hanya daya kawai suka sani: ita ce ta zargi da tsinewa masu aikata zaluncin akan idonsu. To a haka zuriyar da ta biyo baya ta girma cike da fushi da zalunci da yawan tsinewa mutane, kai kace wannan ita ce amsar. Ba su taba tunanin gano cewa jahilci shine babbar matsalar ba. Tabbas, kamar yadda yake cikin kowace al'umma, a wannan al'ummar ma akwai mutane masu muguwar manufa. To amma, in da za a wayar da kan jahilai, wadanada su suka fi yawa a cikin al'ummar, za a rage tasirin wannan muguwar dabi'a. Sai dai kuma, kada a manta cewa za a iya magance jahilci ne ta hanyar kyakkyawan tsarin ilmantarwa da wayar da kai daga wadanda ke amfani da harshen aminci kadai. Yayin da aka kauda jahilci, babu kuma wanda zai yi batun kisa, harba makamin roket ko zama dan kunar-bakin-wake. Fasa bamabamai da kashe kashe za su zama tsohon ya yi. Tabbas, akwai bukatar kyawawan dabi'u da sanin ya kamata don tabbatar da dauwamar harshen aminci a cikin al'ummar da ta ke rayuwa kan barna da zalunci. To amma ana iya warware matsala ne a mawuyatan lokuta ta juriya da jajircewa. Ilmantar da 'yan ga-ni-kashe-ni da harshen aminci shine mafita. Ko suna so ko ba sa so, wannan shine mafita.

Alkur'ani Ya Haramta Kashe Kai (Yin Kunar-bakin-wake)

kundaklama, bombalama

Kudus, wadda birni ne mai tsarki ga Musulmai, Yahudawa da kuma Kiristoci, wajibi ne ta kasance wurin da duk masu imani za su taru su ambaci Allah cikin farin ciki da soyayya.

Wani kuma muhimmin al’amari da ya taso a lokacin farmakin ‘yan ta’adda da suke yi da sunan addini shi ne na harin kunar-bakin-wake. Wasu mutane da suka jahilci musulunci suna yin maganganu bisa kuskure cewa wai musulunci, wanda yake addini ne na zaman lafiya da soyayya, ya halasta harin kunar-bakin-wake, bayan kuwa a musulunci kashe kai da kuma kisan sauran mutane duk haramun ne. A ayar da take cewa, “Kada ku kashe kawunanku,” (Alkur’ani, sura 4, aya 29) Allah ya bayyana mutuwar kashe kai a matsayin zunubi. A musulunci haramun ga mutum ya kashe kansa ko kanta, akan kowane irin dalili.

Kashe kai da kuma kai harin kunar-bakin-wake, da nufin salwantar da rayukan dubban mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, ya sabawa koyarwar musulunci. Allah Yana fada a cikin Alkur’ani cewa aikata zunubi ne mutum ya dauki ransa da kansa ko ran wasu daban. Saboda wannan dalili, abu ne mai wuya ga mutumin da ya yi imani da Allah kuma yake ikrarin aiki da Alkur’ani ya aikata wannan danyen aiki. Jahilai wadanda ba su fahimci addini ba, wadanda ba su san koyarwar Alkur’ani ba kuma ba sa aiki da kwakwalwarsu, su ne kadai za su iya aikata wannan. Su ne wadanda zindikai suka wanke musu kwakwale suka cusa musu ra’ayin kiyayya da daukar fansa. Dole ne kowa da kowa ya yaki wannan barna.

"Kada ku kashe kawunanku,"
(Alkur'ani, sura 4, aya 29)

Tattaunawa tare da Adnan Oktar

Dole Musulmai Su yi Gwagwarmaya Ta hanyar Ilimi da Hujjoji

Dan jarida: Shin ko za ka yi takaitaccen bayani akan ta'addanci? Ana ta kai harin kuna-bakin-wake a kasar Afghanista. Shin ya halatta a musulunci? Shin za a yin jihadi ta hanyar kashe kai?

Adnan Oktar: Meye abin nema a kunar-bakin-wake? Abu daya shine kunar-bakin-wake aikin zunubi ne. Kashe mutum haka kawai babu dalili abu ne da ke da hukuncin dauwama a wuta. Duk wanda ya kashe kansa to ya kashe mutum ne kuma ya aikata babban zunubi, sannan kuma tun da ya mutu ba tare da ya tuba ba zai iya dauwama a wutar jahannama. Saboda haka, ya kamata musulmi ya ilmantar da kansa, maimakon kashe kansa, sannan ya habaka ilimi, mu'amala, karfi, tausayi da kuma sonsa ga jama'a, kuma ya fita don fadakar da mutane. Babu bukatar ka je kana jefawa mutane bam. Je ka yi musu wa'azi, ka yi musu bayanin musulunci. Akwai wani lokaci, kamar yadda ka sani, farkon fara kiran Manzon Allah (SAW) kafin ya fara kira a sarari. Sun fara kira ne a sirri, sannan daga baya suka fito fili. Sun sha bakaken maganganu, zalunci, duka da zagi, an ware su aka hana hulda da su, kuma har ta kai ga sun tsallake sun bar kasar haihuwarsu suka yi hijira zuwa wata kasar. A cikin wannan hali na kunci da tsangwama suka rika yin kira, kuma haka duk musulmai ya kamata su gudanar da da'awarsu, wa'azi da fadakarwa. Amma jefa bamabamai da rataye mutane ba zai amfanar da komai ba. Wannan ba daidai ba ne. Ya yi hannun riga da Alkur'ani, kyawawan dabi'un Alkur'ani da kuma dalilan hankali.

Da za su bude makarantu, masha Allahu, wannan abu ne mai kyau. Su je su yi ta koyar da addinin da ilimin kimiyyya. Suna iya shiga yaki da akidar Darwiniyanci su rushe falsafarsa tare da shirya matakan amfani da ilimi wajen kalubalantar akidun Markisanci, Leniyanci, kwaminisanci da farkisanci. Su tashi su daga matsayin al’adarsu, su yi shiga ta mutunci mai tsafta sannan su yada kyakkyawar dabia a ko’ina. Wannan ita ce hanyar yada musulunci. Amma ba musulunci ba ne zubar da jinin mutane haka kawai, jefa musu bamabamai da ragargaza su. Wadannan abubuwa ne da Manzon mu (SAW) bai ce a yi ba, kuma ba su da gurbi a Alkur’ani, munanan abubuwa ne da aka shigo mana su daga baya. Su kuma suna ta aikata zunubi da wannan munanan ayyukan. Abin da ya dace a yi shine a maida wadannan makarantu tamkar lambuna na aminci. A kafa kyawawan makarantu na zamani don koyarwa da wayar da kan mutane, ko ba haka ba? Don yada, soyayya, aminci, ‘yan uwantaka, mutumtaka, kwazo da son taimakawa jama’a, a takaice, a koyar tare da yada kyawawan dabi’u. Ba za ka iya yada addini ba ta hanyar jefa bamabamai, wannan yakan haifar da kishiyar sakamako ne. Ta’addanci bala’I ne. Amma addini zai bunkasa ta hanyar irin al’amuran dana bayyana wanda kuma hakan zai sanya dabi’un musulunci su mamaye duniya baki daya, insha Allah. (Afghanistan Ayna, 12 ga Disamba 2008)

'Yan harin Kunar-bakin-wake Suna Yada Gurbataccen Musulunci Ne

Me ke sa mutum ya zama dan harin kunar-bakin-wake?

A bayan Yakin Duniya na biyu akidar gurguzu ta yi matukar tasiri a mafi yawan kasashen larabawa. Kungiyoyi irinsu Jam'iyyar Ba'ath da ta yi karfi a kasashen Masar, Siriya da Iraki, da gungun Shanghai wadda kungiyar kasashe ce masu biyayya ga kasar Chaina da ta kunshi kasashen larabawa da Iran, da kuma kungiyar Fatah da ta ginu karkashin jagorancin Yasser Arafat, ba su taba boye akida da kuma biyayyarsu ga tsarin gurguzu ba. Ba boyayyen abu ba ne cewa hadakar akidar kwaminisanci da ta tsananin kishin kasa sun haddasa rikici da zubar da jini a kasashen larabawa. Ya kamata wadanda suka san tarihi su halin wadannan kasashe yanzu ko kuma yadda ake tafiyar da mulkin da Hafiz Assad ya assa a kasar Siriya.

Irin wannan ta'addanci ba bako ba ne wajen 'yan gurguzu. A irin wannan ra'ayi, mutum ya kashe kansa daidai yake da bayar da babbar gudunmuwa ga cigaban duniya da kuma cigaban "manufa" daidai kuma da daukar ran wani mutum. Saboda haka, mutum ya dauki ransa, wanda yake ganin ba shi da muhimmanci, don ya kaashe rayukan wasu mutane, wadanda yake ganin ba su da amfani, ba karamin aikin sadaukarwa ba ne a cikin wannan akida ta ta'addanci. Wannan abu ne da ya sabawa hankali, amma maudu'i ne na wani lokacin.

Idan dan harin kunar-bakin-wake zai rika aiwatar da ta'addancinsa da sunan Musulunci, to wannan ba karamin cin mutunci ba ne. Akwai babban kuskure a nan. Musulmi ba ya kisa. Wannan zunubi ne. Allah yana fada a cikin Alkur'ani cewa "…Lalle ne wanda ya kashe rai ba da wani rai ba, ko barna a cikin kasa, to kamar ya kashe dukkan mutane ne." (Alkur'ani, sura ta 5, aya ta 32) A yar ta yi bayani filla filla. Kamar yadda yake zunubi da kisan kai mutum ya kashe wani daban, to haka yake zunubi da kuma kisan kai in mutum ya kashe kansa. Ba jihadi ba ne mutum ya shiga gidan abinci ya tayar da bam. Wannan aikin zunubi ne. Wadanda ke girmama wannan aika aika suke tsammanin mutumin da ya aikata hakan ya yi shahada, suna goyon bayan kisan kai ne kawai, ba jihadi ba.

Jihadi yana nufin yin kokari ta hanyar ilimi da kimiyya don nunawa mutane gaskiya tare kuma da bude kyakkyawar hanyar sadarwa ta mu'amala da ke jawo soyayya da girmama juna, amma ba kashe mutane ba. Shahada tana nufin mutum ya mutu yayin da yake kokari a tafarkin Allah inda yake kokarin yada soyayya, abota da kuma 'yan uwantakar da musulunci ya koyar. Kisa ta'addanci ne kuma aikin zunubi. Ba wani aikin kwarai ba ne da za a girmama mai yinsa.

Amma su 'yan harin kunar-bakin-wake da masu goya musu baya sukan yada farfagandar cewa addini ne ya halatta kashe wasu mutane. Muna iya cewa addinin da suke fada ba addinin Allah ba ne. Sai dai kadan ne daga cikinsu za su iya gane haka. Wakilan kungiyar da suke ganin daidai ne su girmama 'yar karamar yarinyar da 'yan ga-ni-kashe-ni suka cusawa ra'ayin zama 'yar kunar-bakin-wake da ke hallaka bayin Allah, ba lalle ne su san wannan gaskiyar ba. Akwai mutane masu yawa da suke daukar wannan gurbataccen addini a matsayin shine daidai har kuma suke neman koyi da shi.

Matsalar ita ce: Mutanen da ba su fahimci addininsu ba su ake kautarwa zuwa wannan haukar. Kuma in dai har mutane ba su tsaya sun karanci addininsu da kuma kyakkyawar koyarwar Alkur'ani ba, to za a ci gaba da samun 'yan kunar-bakin-wake da masu goyon bayansu. Kuma jefa musu bam ba shine zai koya musu gaskiya ba; hanya daya ita ce sahihin ilimi. Kuma in har ana son samar da wannan sahihin ilimi, to sai mutane masu hankali daga cikin musulmai, kiristoci da yahudawa sun hannu wuri daya. Da zarar an sami karfin hadin kai, sannan ne mutanen da suke bin hanyar bata za su fara sauraron abin da mu ke fada musu.

Jin kai, Kauna da kuma Mutumtaka a Tarihin Musulunci

In za mu takaice bayanai da hujjojin da muka gani zuwa yanzu, za mu iya cewa musulunci addini ne na zaman lafiya, soyayya da kuma jin kai. Wannan al'amari ne da masana tarihi da malaman addini wadanda ba musulmai ba suka amince da shi. Daya daga cikin wadannan mutane ita ce masaniyar tarihi 'yar kasar Birtaniya, Karen Armstrong, wadda kuma tsohuwar fadar coci ce kuma kwararriya akan tarihin Gabas Ta tsakiya. A cikin littafinta mai suna Holy War (Yakin Addini), wanda ya yi nazarin tarihin saukakkun addinan nan guda uku, ta gabatar da wadannan bayanai:

… Kalmar 'Musulunci' ta fito ne daga asalin larabci daya da kalmar 'aminci ko zaman lafiya' sannan kuma Alkur'ani ya la'anci yaki a matsayin wani bataccen yanayi da ya sabawa kudurin Allah… Musulunci bai halatta yakin zalunci na ganin bayan al'umma ba… Musulunci ya yarda cewa yaki wani abu ne da ake yinsa in ya zama ba makawa sai an yi shi wanda kuma yake da amfani wani lokaci don kauda zalunci da fitar da al'umma daga kunci. Alkur'ani yana nuna cewa yaki dole ne ya zama kan ka'ida kuma a aiwatar da shi da taka-tsantsam da kare hakkin mutane. Ba mutanen Makka kadai Mohammad ya yaka ba, har da kabilun yahudawan yankin da kuma kabilun kiristoci a Sham wadanda suka hada kai da Yahudawa don yi masa taron dangi. Amma wannan bai sa Mohammad ya tsani Ahlul Kitabi ba. Musulmai mabiyansa sun gwabza yaki ne don kare kansu ba wai suna 'jihadi' ne don rushe addinin makiynasu ba. Lokacin da Mohammad ya tura 'yantaccen bawansa Zaid don ya yaki Kiristoci a matsayin jagoran rundunar musulmai, ya gaya musu cewa su yi yaki a tafarkin Allah da jaruntaka kuma su lura da hakkin mutane. Kada su taba malaman addini, masu bauta da kuma mata masu hidimar addini haka nan da raunana da marasa karfi wadanda ba za su iya yaki ba. Ban da kisan kare dangi akan talakawa haka kuma kada su sare koda bishiya daya sannan kada su rushe koda gini guda.4

Halifofin da suka zo bayan Ma’aiki Muhammad (SAW) su ma sun kasance masu kaffa kaffa wajen aiwatar da adalci. A kasashen da aka ci da yaki, gaba daya da ‘yan asalin kasar da kuma wadanda suka shigo duk sun ci gaba da harkokinsu cikin aminci da tsaro. Abubakar (ra), Halifa na farko, ya hori mutanensa da su aikata halayen adalci da jin kai a wadannan kasashe. Kuma duk wadannan halaye daidai suke da abin da Alkur’ani ya koyar. Kafin sojojin musulmai su fita zuwa fagen daga a Sham karo na farko, Halifa Abubakar ya karanta musu wadannan dokoki:

Ku dakata, ya ku mutane, zan gaya muku wasu dokoki goma don ku hardace su: Kada ku juya baya ga rundunarku, haka na kada ku kauce daga tafarki. Kada ku daddatsa gawa, kuma kada ku kashe yaro ko tsoho ko mace. Kada ku sare ko kona bishiyar dabino, sannan kada ku yanke duk wata bishiya mai amfani. Kada ku yanka dabobi ko rakuma, ku ajiye su don amfaninku. Da alama za ku wuce ta wajen mutanen da suka kebe kansu cikin dakunan ibada suna bauta; ku kyale su akan abin da suke yi. Haka kuma za ku iya haduwa da wasu mutane da za su baku abinci kala kala. Kuna iya cin abincin; amma kada ku mance da ambaton sunan Allah.5

Umar dan Khaddabi, wanda ya gaji Abubakar, ya kasance sunansa ya shahara akan yadda ya gudanar da adalci da yadda ya kulla yarjejeniya da asalin mutanen kasashen da ya ci da yaki. Kowace daya daga cikin wadannan yarjejeniyoyi ta kasance misalia jin kai da kuma adalci. Misali, a sanarwar da ya yi ta bada kariyar tsaro ga Kiristocin da ke biranen Kudus da Lod, ya bayar da tabbacin cewa ba za a rushe coci ba sannan kuma ya bayar da tabbacin cewa musulmi ba za su yi ibada cikin coci a jam'i ba. Sayyidina Umar ya bayar da irin wannan kariya ga Kiristocin da ke Bethlehem. Haka nan, lokacin da Musulmai suka ci birnin Mada'in da yaki, sanarwar kariya da aka baaiwa shugaban darikar kirista ta Nastoriya, Isho'yab na uku (650-66 shekarar kirista) har ila yau tab a tabbacin cewa ba za a rushe coci ba sannan da cewa babu wani gini da musulmai za su maida shi gidansu ko masallaci ba 6Wasikar da shugaban darikar ya rubutawa babban limamin kirista na Farisa bayan kama garin abin burgewa ce, inda ta ke nuna bayanin fahimta da kuma jin kai da shugabannin musulmi ke nunawa Ahlul Kitabi da ke karkashin mulkinsu daga bakin Kirista:

Larabawa wadanada Allah ya damka mulkin duniya a hannunsu… bas a kuntatawa addinin kirista. Hasali ma, sun yi wa addini gata, suka karrama malaman addininmu da waliyan Allah sannan suna bayar da gudunmuwa ga coci coci da gidajen masu bauta.7

Wannan rubutu na kasa daga Umar yana nuna mana irin fahimta da kuma tsarin adalci da Allah Ubangiji ya baiwa dan Adam, matukar zai rungumi dabi’ar halayya da aka bayyana a cikin Alkur’ani:

Wannan kariya ce, wadda bawan Allah, sarkin muminai Umar, ya baiwa mutanen Elia. Yana bayar da tabbaci ga kowa, mai lafiya da marar lafiya, na tsaron rayukansu, dukiyoyinsu, dakunan bauta da sakandamansu, da duk abin da ya shafi addininsu. Ba za a maida dakunan bautarsu gidajen kwana ko a rushe su ba, ba za a wulakanta su ko abin da suka mallaka ba, haka da sakandaman mutanen garin ko wani abu daga dukiyarsu, ba za a sanya musu nakasu a ko a cikin al'amarin addinisu ba, haka kuma ba za a cutar da kowane daya daga cikinsu ba.8

Duk wadannan muhimman misalai ne da ke nuna fahimtar adalci da sanin ya kamaya na masu imani na kwarai. A wata aya Allah yana bada umarni cewa:

Lalle ne Allah Yana umarninku da ku bayar da amanoni zuwa ga masu su. Kuma idan za ku yi hukunci a tsakanin mutane, ku yi hukunci da adalci. Lalle madalla da abin da Allah yake yi muku wa'azi da shi. Allah Ya kasance Mai ji ne, Mai gani.
(Alkur'ani, sura ta 4, aya ta 58)

Canon Taylor, daya daga cikin shugabanni a Cocin Angilikan, ya bayyana kyawun dabi’ar tsarin musulunci a daya daga jawabansa kamar haka:

[Musulunci] ya fito da muhimman akidun addini – kadaitaka da girman Ubangiji, cewa Shi Mai rahama ne da gaskiya, cewa Yana bukatar biyayya ga kudurinSa, mika wuya da imani. [Adinin] ya yi bayanin nauyin da ked an Adam, rayuwa mai zuwa, ranar sakamako, sannan da mummunar azaba akan mugayen mutane; sannan ya wajabta ayyuka na sallah, zakkah, azumi da taimakon jama'a. Ya yi watsi da dabi'un karya, zambar addini da halayen banza, dabi'un fasikanci, da kuma maganganun burgewa na masu musun addini… Ya sanya fatan 'yanci ga bawa, 'yan uwantaka ga 'yanAdam, sannan ya tabbatar da gaskiyar al'amuran dabi'ar mutum.9

Radikalizm, terör

Yawancin 'yan salibiyya sun yi mamakin halayyar adalci da tausayi da Musulmai suka nuna hatta a filin yaki. Daga baya sun bayyana sha'awarsu kan wannan halayya cikin rubuce rubucensu. A hoton da ke kasa za mu ga yakin Salibiyya na biyu wanda Louis Na Bakwai ya kaddamar.

Masu bincike na Yammacin Turai sun karyata maganar da ake cewa wai an tilastawa mutane shiga musulunci a kasashen da musulmai suka ci da yaki, inda hakan ya kara tabbatar da halayyar musulmai adalci da jin kai. Wani mai bincike dan Yammacin Turai, L. Browne, ya bayyana wannan lamari a wadannan kalmomi:

Kuma a hakika wadannan kwararan hujjoji sun rusa ra'ayin da aka dade ana yadawa a rubuce rubucen Kiristoci da ke cewa wai musulmai duk inda suka je suna tilastawa mutane karbar musulunci da tsinin takobi.10

kan dökmek, cinayt

Mulkin Musulmai a Spain ya zo karshe cikin 1492 lokacin da rundunonin Sarki Ferdinand da Sarauniya Isabella suka kame Granada. A hoton da ke sama, an nuna faduwar birnin.

Browne ya ci gaba da fada, a littafinsa mai suna The Prospects of Islam, cewa babbar manufar yakukuwan musulmai ita ce yada ‘yan uwantakar musulunci. Mafi yawan musulmin da suka yi mulki a kasashen musulmai a tsawon tarihi sun rika baiwa mabiya sauran addinai matukar kulawa da girmamawa. Duka Yahudawa da Kiristoci sun rayu cikin aminci a kasashen musulunci tare da samun ‘yancin walwala.

Haka ma daulolin Seljuk da Ottoman sun shahara wajen mulkin musulunci mai cike da ‘yanci da jin kai. Thomas Arnold, a cikin littafinsa mai suna The Preaching of Islam, ya bayyana yadda Kiristoci ke son su dawo karkashin mulkin Seljuk saboda irin wannan hali:

Wannan yanayin amincin rayuwar addini karkashin mulkin Musulmai ya sanya da yawa daga Kiristocin yankin Karamar Asiya, a daidai wannan lokaci, yin murna da zuwa Turkawan Seljuk a matsayin masu ceton su… A lokacin mulkin sarki Michael Na Takwas (1261 – 1282), mazauna kananan garuruwan da ke tsakiyar Karamar Asiya sun sha gayyatar Turkawa don su mamaye garuruwan, da nufin su guje wa bakin zaluncin daular da suke karkashinta; kuma talakawa da masu arziki sun rika kaura suna komawa yankunan da ke karkashin Turkawa.11

Malik Sha, wanda ya mulki Daular Musulunci ta Seljuk lokacin ganiyar tashenta, ya gudanar da al’amuran jama’ar kasashen da ya ci da yaki cikin adalci da nuna jin kai, inda hakan ya sa suke tuna shi da girmamawa tare da soyayya. Dukkan marubuta tarihi masu adalci sun ambaci Sha cikin rubuce rubucensu. Haka nan, jin kai da kyautatawarsa sun sa soyayyarsa a zukatan Ahlul Kitabi. Saboda wannan dalili ya sa, abin da ba a taba gani ba a tarihi, birane da yawa suka shigo karkashin mulkin Malik Sha don radin kansu. Haka kuma Sir Thomas Arnold ya ambaci Odo de Diogilo, wani mai bauta a St. Denis, wanda aka yi yakin Salibiyya Na biyu da shi a matsayin limamin addini na sarki Louis Na Bakwai, wanda a labarin rayuwarsa da ya rubuta ya yi tsokaci ga tsarin adalcin da Musulmai suka aiwatar ba tare da la’akari da addinin mutum ba. Daga cikakken labarin da Odo de Diogilo ya bayar, Sir Thomas Arnold ya rubuta cewa:

Da al'amarin wadanda suka tsira da kansu ya tabarbare, ba don ganin halin da suke ciki ya narkar da zuciyar Musulmai da tausayi ba. Suka yi wa marasa lafiya magani sannan taimakawa talakawa da wadanda yunwa ta kusa kashewa cikin fara da saukin kai. Wasu daga cikinsu ma sun canji kudin faransa wanda Girkawa suka karbe daga masu ziyarar ibada ta karfi ko dabara, sannan suka rarrabawa mabukata. Akwai babban bambanci tsakanin jin kai da karramawar da masu ziyarar ibada suka samu daga [gurinsu]… da kuma keta da muguntar 'yan uwansu Kiristoci, Girkawa, wadanda suka tilasta su aikin wahala, da dukansu, sannan suka kwace musu dan abin da ya rage garesu, inda hakan ya sa da yawansu suka zabi shiga addinin mutanen da suka ceto su. Kamar yadda tsohon marubucin tarihin [Odo de Diogilo] ya ke cewa: "Bayan sun guje wa 'yan uwansu na addini wadanda suka dinga gana musu azaba, sai suka sami aminci da tsaro a wajen kafirai wadanda suka ji kansu, kuma kamar yadda muka ji, sama da dubu uku suka hade da Turkawa lokacin da suka koma gida.'12

kan dökmek, cinayt

Sultan Beyazid ya kasance mai rikon addini. Ya karbi Yahudawan da suka gujewa kuntatawa a Spain, inda ya ba su 'yancin gudanar da al'amuran addinisu a garuruwan musulmai.

Wannan bayani daga marubuta tarihi yana nuna cewa shugabannin musulmai wadanda suka riki kyakkyawar koyarwar musulunci koda yaushe sukan tafiyar da mulkinsu akan jin kai da adalci. Kamar haka kuma, tarihin Daular Ottoman wadda ta mulki kasashe a nahiyoyi uku na tsawon karnoni, cike yake da misalan adalci.

Yadda Yahudawa suka sami gindin zama a garuruwan Ottoman a zamanin Sultan Beyazid Na Biyu, bayan sun sha kisan kare-dangi da kuma kora a masarautu masu bin Cocin Katolika da ke kasashen Spain da Portugal, kyakkyawan misali ne na jin kai da tsarin musulunci ya zo da shi. Sarakuna mabiya Katolika wadanada suke mulkin yawancin kasar Spain a lokacin sun tsanantawa Yahudawa wadanda kafin nan suka zauna cikin aminci karkashin mulkin Musulmai a Andalusiya. Sarakunan Katolika sun yi kokarin tursasawa kowa a kasar ya zama kirista, inda suka kulla yaki akan musulmi yayin kuma da suke cigaba da zaluntar Yahudawa. Sakamakon haka, an kifar da gwamnatin musulmai ta karshe a yankin Girnada na kudancin Spain a shekarar 1492. An yi ta yanka musulmi ba kakkautawa, su kuma yahudawan da suka ki yarda su bar addininsu aka kora su gudun hijira.

Wata kungiya daga cikin wadannan yahudawa da aka kora ta nemi mafaka a Daular Ottoman, kuma gwamnati ta ba su izinin zama. Rundunar sojan ruwan Ottoman karkashin jagorancin Kemal Reis, sun dauko yahudawan da aka kora da kuma musulmai da suka tsira daga kisan gilla, zuwa yankin kasar Ottoman.

Sunan Sultan Bryazid Na Biyu ya shiga tarihi a matsayin cikakken mai imani, inda a daminar shekarar 1492 ya saukar da wadannan yahudawan da aka zalunta aka koro su daga Spain a wasu bangarori na daularsa, a wajejen Edirne da Thessalonica da ke cikin kasar Girka ta yanzu. Mafi yawan Yahudawa Turkawa dubu ashirin da biyar da ke zaune yanzu a Turkiyya jikokin wadancan yahudawan Spain din ne. Sun rika aiwatar da addini da al’adunsu wadanda suka zo da su daga Spain tun kimanin shekaru 500 da suka wuce kuma har yanzu suna cigaba da rayuwarsu cikin jin dadi tare da makarantunsu, asibitoci, gidan tsofaffi, kungiyoyin al’adu da kuma jaridu. Haka kamar yadda suke da kanana da manyan ‘yan kasuwa, to kuma suna da wakilai a bangarorin sana’a daban daban, daga ayyukan fasaha zuwa talla, tare kuma da gungun masana da kullum ya ke fadada. Yayin da al’ummomin Yahudawa a kasashe da dama a Turai na tsawon karnoni suke zaune cikin fargabar hare haren ‘yan kin jinin yahudu, Yahudawan Turkiyya kuwa suna zaune cikin aminci da tsaro. Wannan misali kadai ya isa ya nuna jin kai wanda musulunci ya zo da shi da kuma fahimtar adalcinsa.

kan dökmek, cinayt

TKwace Istanbul da Sultan Mehmet ya yi ya samar da 'yanci ga Yahudawa da kuma Kiristocin heterodox wadanda suka sha bakar wahala a tsawon karnoni karkashin mulkin sarakunan Roma da Girka. Sultan Mehmet Mai nasarar yaki, ya yi rangwame mai yawa ga Shugabancin addini. Shugaban addinin ya sami 'yancin cin gashin kai a karon farko a tarihi, karkashin mulkin Turkiyya. A wannan hoto za mu ga Sultan Mehmet Mai nasarar yaki yana karbar Shugaban addinin

Jin kai da tausayin da Sultan Beyazid Na Biyu ya bayyanar ya shafi duk sarakunan Ottoman. Lokacin da Sultan Muhammad ‘Mainasara’ ya ci Istanbul da yaki, ya kyale Kiristoci da Yahudawa su zauna ba tare da tsangwama ba. Andre` Miquel, wanda ya yi suna wajen fitattun littattafansa da ya rubuta akan ayyukan adalci da jin kai na musulmai da kuma duniyar musulunci, yana cewa:

Al'ummar Kiristoci sun rayu karkashin kasa mai kyakkyawan jagoranci wanda ba su samu ba lokacin mulkin daular Byzantine da Latin. Ba su taba fuskantar wata kuntatawa da azabtarwa ba. A maimakon haka, daular da kuma musamman Istanbul sun kasance mafaka ga Yahudawan Spain wadanda aka azabtar. Babu inda aka musuluntar da mutane da karfin tsiya; gwagwarmayoyin Tabbatar musulunci sun faru ne sakamakon canje canjen zamantakewa.13

Ko kafin gwamnatin musulunci ta Ottoman ana baiwa wadanda ba musulmi ba dama da ‘yanci rayuwa mai yawa. Farfesan nazarin Addini da Dangantakar Kasashe na Jami’ar Georgetown, John L. Esposito ya bayyana yadda Yahudawa da Kiristoci wadanda suka sami kansu karkashin mulkin kasar musulmai suka sami gagarumar fahimta:

Ga da yawa daga al'ummar da ba Musulmai ba da ke yankunan Byzantine da Farisa wadanda dama suke karkashin mulkin wasu kasashen, mulkin Musulunci yana nufin canjin masu mulki, wanda kuma sababbin sun fi zama masu saukin kai da hakuri, a maimakon rashin 'yanci. Da dama daga wadannan al'ummu yanzu haka sun sami kwarya kwaryan 'yancin cin gashin kai inda mafi yawa sukan biya haraji dan kadan… A addinance, musulunci ya tabbata addini mafi hakurin zama da kowa, inda yake bayar da cikakken 'yanci addini ga Yahudawa da Kiristoci 'yan kasa.14

Kamar yadda ya bayyana daga wadannan hujjoji, babu inda musulmi suka zama azzalumai a tsawon tarihi. A maimakon haka ma, sun samar da aminci da tsaro ga kasashe da addini a duk inda suka shiga. Sun yi aiki ne da ayar Allah wadda take cewa: “Ku bauta wa Allah, kuma kada ku hada wani da Shi, kuma ga mahaifanku ku yi kyautatawa, kuma ga ma’abocin zumunta da marayu da matalauta,da makwabci ma’abocin kusanta, da makwabci manisanci, manisanci, da aboki a gefe da wanda ke kan hanya, da abin da hannuwanku na dama suka mallaka. Lalle Allah ba Ya son wanda ya kasance mai takama, mai yawan alfahari.” (Alkur’ani, sura ta 4, aya ta 36) kuma suka yi kyakkyawar mu’amala da kowa.

A takaice, abota, ‘yan uwantaka, zaman lafiya da soyayyar juna sune gishikan tarbiyyar Alkur’ani, kuma wadannan madaukakan dabi’u ne Musulmai suke kokarin dabbakawa. (Don samun cikakkun bayanai, duba littafin Harun Yahya mai suna Justice and Compassion in the Qur’an)

Wadanda suka yi imani kuma ba su cudanya imanisu da zalunci ba, wadannan su ne ke da aminci…
(Alkur'ani, sura 6, aya 82)

Tattaunawa tare da Adnan Oktar

Wajibi ne Musulmai su yi Koyi da Kyautatawar Annabinmu (SAW)

Adnan Oktar: Ahlul Kitabi wani fitaccen maudu'i a cikin Alkur'ani. Ba bakon abu ba ne. Wasu jahilan mutane suna da mummunar fahimta akan Ahlul Kitabi, suna ganin "ya kamata a kashe su duk inda suke, a jefa musu bam a duk inda aka gansu. A kai hari wajen bukukuwansu a kashe kowa da kowa, ba yaor ba mace." Sai dai wannan aikin zunubi ne. Babu gurbin wannan aika aika a musulunci. Musulunci ya kunshi kyautatawa da jin kai. An danka mana amanarsu ne. Insha Allah, za su kasance karkashin tsaro da kulawarmu a lokacin Hadaddiyar Daular Musulunci ta Turkiyya. Duba wannan, daga takardar yarjejeniya tsakanin Kiristoci da Musulmai a zamanin Sayyidina Umar (ra). Yarjejeniya tsakanin Musulmai da Kiristocin Hira tana cewa: "Idan daya daga cikinsu ya zama mai rauni – kowanne daga Kiristocin – ko tsufa ya zo masa ko marar lafiya, ko ya talauce bayan da ya kasance mai arziki, to za a ba shi ko iyalinsa tallafi daga Baitul Mali har iya zamansu a kasar Musulunci." Babu wata maganar kisa, yanka, jefa bam ko kuma tsana a nan, ko akwai?

Abin da ake nufi, idan suna danganta kansu ne da zamanin rayuwar Manzon Allah (SAW) da kuma koyarwar Alkur'ani, to abin da suke yi haramun ne. Kamar yadda yake Alkur'ani da Sunnar Ma'aikin Allah (SAW), ga yadda lamarin yake, duba, "idan daya daga cikinsu ya zama mai rauni – kowanne daga Kiristocin – ko tsufa ya zo masa ko marar lafiya, ko ya talauce bayan da ya kasance mai arziki…" abin nufi, wannan ba karamin abu ba ne, ko ba haka ba? An fadada abin har kan mutanensa, amma ta fi maida hankali akan Kiristoci. "… to za a ba shi ko iyalinsa tallafi daga Baitul Mali har iya zamansu a kasar Musulunci." Takardar mika wuya da ka rubuta don Kiristoci, Yahudawa da kuma Masu Bautar wuta da ke zaune a Debil – wani birni a kasar Armeniya – lokacin da musulmai suka kama garin a zamanin halifancin Sayyidina Usman (ra), ta bayar da tabbacin cewa za a bada kariya ga wuraren bauta. An bayar da damar gyara Coci coci da aka lalata, sannan kuma koda yaushe ana bayar da izinin gida sababbin wuraren bautar yahudawa da gidajen ibada. Shugaban addinin yahudawa, Mar Amme, ya sami iznin sake gina wani wurin bautarsu da aka kone daga Sayyidina Usman. Babu jefa bamabamai, ko akwai? Babu kisa da yanka mutane. Haka nan an ba su tabbaci kan garuruwansu da kayayyakinsu. Babu wanda aka matsawa shiga musulunci. Babu kuma wanda ke yin katsalandan a cikin dokokinsu. (Gidan talbijin na Gaziantep Olay, 23 ga Janairu 2010)

Footnotes

2. John L. Esposito, Islam: The Straight Path, Oxford University Press, 1998, p. 10

3. Ahmad Diya'al-Din al-Kamushkhanawi, Ramuz al-Ahadith, Vol 1, 84/8

4. Ahmad Diya'al-Din al-Kamushkhanawi, Ramuz al-Ahadith, Vol 1, 76/12

5.Bukhari (5778) da Muslim (109 and 110), Reported by Muslim - Eng. Trans, Vol. 1, p.62, No. 203

6. Karen Armstrong, Holy War, MacMillan London Limited, 1988, p. 25

7.Tabari, Ta' rikh, 1, 1850, da aka ambata a Majid Khadduri, War and Peace in the Law of Islam, Johns Hopkins Press, Baltimore, 1955, p. 102

8. W.H.C. Frend, "Christianity in the Middle East: Survey Down to A.D. 1800", Religion in the Middle East, Ed. A.J. Arberry, I-II Cambridge, 1969, Volume I, p. 289

9. Prof. Thomas Arnold, The Spread of Islam in the World, A History of Peaceful Preaching, p. 71-72

10.L. Browne, The Prospects of Islam, p. 11-15

11.John L. Esposito, Islam: The Straight Path, p. 33-34

12.Bernard Lewis, The Middle East, Weidenfeld & Nicolson, London, 1995, p. 210

13.Prof. Thomas Arnold, The Spread of Islam in the World, A History of Peaceful Preaching, p. 96

14.Prof. Thomas Arnold, The Spread of Islam in the World, A History of Peaceful Preaching, p. 88-89