GABATARWA

11 eylül, terörist saldırı
Allah commands justice and doing good and giving to relatives. And He forbids indecency anddoing wrong and tyranny. He warns you so that hopefully you will pay heed.
(Surat an-Nahl, 90)

A matsayinmu na musulmi, muna yin Allah-wadai da dukkan hare haren ta’addanci a fadin duniya. Wadanda suka hada da harin da aka kai kan manyan biranen kasar Amurka biyu a ranar 11 ga Satumban 2001, wanda ya jawo mutuwa da kuma jikkatar dubban mutane wadanda bas u jib a bas u gani ba.

Harin 9/11 ya kawo muhimmancin duba al’amarin tushen ta’addanci a duniya. Don haka, aka shelantawa duniya baki daya cewa musulunci addinin zaman lafiya ne da soyayya wanda ke horon daidaikun mutane da nuna tausayi da kuma yin adalci. Da yawan shugabannin kasashe, manyan kafafen watsa labarai irinsu rediyo da talbijin, sun bayyana cewa a musulunci na gaskiya an haramta tashin hankali kuma ana karfafa al’amarin zaman larfiya tsakanin mutane da kasashe. Jama’ar yammacin turai wadanda suka fahimci hakikanin addinin musulunci kuma suka nazarci addinin sosai kamar yadda Allah ya saukar das hi a Alkur’ani sun bayyana balo balo cewa kalmomin “musulunci” da kuma “ta’addanci” ba sa haduwa wuri guda, sannan kuma cewa babu wani saukakken addini da ya amince da tashin hankali.

Wannan littafin yana kara tabbatar da cewa tushen ta’addancin da muke la’anta ba daga saukakken addini yake ba, da kuma cewa ta’addanci bas hi da gurbi a musulunci. Wannan ya zo karara a cikin Alkur’ani da hadisai, wadanda sune manyan mahangun musulunci, da kuma a ayyuka da rayuwar dukkan shugabannin musulunci na kwarai, wanda na farkonsu shine Manzo Muhammad (SAW). Wannan littafi yana bayani, ta mahangar ayoyin Alkur’ani da kuma sunnar manzonmu Muhammad (saw) tare da misalai da tarihi, cewa an haramta ta’addanci sannan kuma manufar musulunci it ace tabbatar da aminci da tsaro a duniya.

terör, savaş

Idan mutum yana neman abin da ke haddasa aikin ta'addanci, mutum zai nemi asalinsa ne a akidun kin addini. Addini yana horo da nuna soyayya, tausayi, afuwa, zaman lafiya da kuma rayuwa kan kyawawan dabi'u. Ta'addanci kuwa, a bangare guda, ya bangaren keta da ta'asa, illata mutane, zubar da jini da kuma aikata kisan kai.

Kamar yadda aka sani a karnoni masu yawa, an kaddamar da ayyukan ta’addanci a sasssa daban daban na duniya wanda kungiyoyin ‘yan ta’adda mabambantan manufofi suka sha yi. A wasu lokutan kungiyar ‘yan gurguzu ce, wani sa’in kuma ‘yan akidar farkisanci ne, sannan a wasu lokutan kuma bangarorin masu tsattsauran ra’ayi da na ‘yan aware ne ki ikrarin wadannan ayyuka. Koda yake wasu kasashe kamar Amurka sun kasance wuraren hare haren ‘yan wariyar launin fata da kuma kananan kungiyoyin ‘yan ta’adda, kasashen turai sune cibiyar ayyukan kashe kashe da kungiyoyin ‘yan ta’adda ke gudanarwa. Kungiyar 17 ga Nuwamba (17th November) a kasar Girka, bangaren Red Army da kuma ‘yan ra’ayin farfado da akidar Nazi a Jamus, kungiyar ETA a Spain, Red Brigades a Italiya da sauran kungiyoyi masu yawa sun hallaka mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ta hanyar ta’addanci da kashe kashe. Yanayin ta’addanci kan canja ne daidai da canjawar halayyar duniya yayin da yake kara karfi da tasiri ta hanyar sababbin kayan kirkirar fasaha. Atakaice, kayan watsa labarai da bayanai irinsu intanet sun kara girma da kuma karfin tasirin ayyukan ‘yan ta’adda ba kadan ba.

Banda na yammacin turai, akwai kuma kungiyoyin ‘yan ta’adda masu tushe a gabat ta tsakiya. Wadannan gungun ‘yan ta’adda sukan kaddamar da hare hare a kowane lungu a fadin duniya. Ganin cewa masu aikata ayyukan ta’addancin suna dauke da sunan kirista, musulmi ko bayahude shi ke sa wasu mutane su rika ikrarin abin da bai dace da saykakkun addinai ba. Gaskiyar lamari dai shine koda ‘yan ta’addar suna da sunayen musulmi ne, to hakan ba zai sa a kira ta’addancin da suke aikatawa ba da sunan “ta’addancin musulunci,” kamar yadda ba za a kira shi da “ta’addancin yahudanci” ba idan masu aikatawar yahudawa ne ko kuma ta’addancin kiristanci idan kiristoci ne. Wannan kuma saboda, kamar yadda za a fahimta a cikin wannan cewa: ba a yarda da aikata kisan gilla akan bayin Allah da sunan saukakkun addinai ba. Ya kamata mu tuna a ranmu cewa, a cikijn wadanda aka kashe, misali a biranen New York da Washington a ranar 9/11, akwai mabiya Annabi Isa (AS) (kiristoci), Annabi Musa (AS) (yahudawa) da kuma Annabi Muhammad (SAW) (musulmai). In dai ba Allah ne ya yafewa mutum ba kisan bayin Allah babban zunubi ne da ke kai mutum wutar jahannama. Babu wani ma’abocin addini, wanda kuma ke son Allah da tsoron azabarsa, da zai aikata irin wannan aiki.

Maharan su kan aikata irin wannan barna ne da niyyar rusa shi kansa addinin. Don haka ana iya cewa wadanda ke aikata ayyukan barnar suna yin haka ne da nufin su bata sunan addinin a ido mutaen, don su nisanta mutane daga addini sannan su sanya kiyayya ga wadanda suke ahalin addinin. A sakamakon haka, duk wani hari akan jama’ar Amurka ko wasu bayin Allah na daban wanda aka fake da sunan addini to hakika hari ne akan addinin.

Addini yana umurni da soyayya, jin kai da kuma aminci. Shi kuma ta'addanci a daya bangaren, kishiyar addini ne; cike yake da mugunta, rashin tausayi da neman zubar da jini da jawo bala'i. To tunda kuwa haka abin yake, za a nemi tushen aikin 'yan ta'adda ne a cikin rashin addini ba a cikin addini ba. Mutane da tunaninsu na rayuwa ya ginu akan akidar farkisanci, kwaminisanci, wariyar launin fata ko son abin duniya sune za a zarga a matsayin masu aikata ta'addanci. Suna ko inda dan ta'addar ya fito ba shi ne abin lura ba. Idan har zai kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ba tare da ya ji gezau ba, hakan ya nuna shi zindiki ne ba mai addini ba. Dan ta'adda ne da ba ya tsoron Allah, wanda babban burinsa shine ya zubar da jini tare da yin ta'annati. Saboda wannan dalili batun "ta'addancin musulunci" kuskure ne kuma ya saba wa sakon musulunci. Babu yadda za a yi addinin musulunci ya kunshi ta'addanci a cikinsa. Sabanin haka ma, ta'addanci (wato kisan mutane da su ji ba ba su gani ba) babban zunubi ne a musulunci, kuma hakki ne akan musulmi da su kawo karshen wannan aiki tare da tabbatar da aminci da adalci a duniya baki daya.

Ku ci ku sha daga arzikin Allah kada ku tafi kuna masu barna a bayan kasa
(Alkur'ani, sura 2 aya 60)