Qaf - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. ¡̃. Inã rantsuwa da Alƙur`ãni Mai girma.
-
2. Ã`a, sun yi mãmãki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yã zo musu, sai kãfirai suka ce: "Wannan wani abu ne mai ban mãmãki."
-
3. "Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓãya (zã a kõmo da mu)? Waccan kõmowa ce mai nĩsa."
-
4. Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwo daga gare su, kuma wurinMu akwai wani littãfi mai tsarẽwa.
-
5. Ã`a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lõkacin da ta je musu, sabõda haka sunã a cikin wani al`amari mai raurawa.
-
6. Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samã a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma Muka ƙawãce ta, kuma bã ta da waɗansu tsãgogi?
-
7. Da ƙasã, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jẽfa kafaffun duwãtsu a cikinta, kuma Mun tsirar, a cikinta daga kõwane ma`auri mai ban sha`awa?
-
8. Dõmin wãyar da ido da tunãtarwa ga dukan bãwa mai tawakkali?
-
9. Kuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa`an nan Muka tsirar game da shi (itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbẽwa.
-
10. Da itãcen dabĩno dõgãye, sunã da`ya`yan itãce gunda mãsu hauhawar jũna.
-
11. Dõmin arziki ga bãyi, kuma Muka rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar wannan ne fitar daga kabari kake.
-
12. Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma`abũta Rassi, da Samũdãwa.
-
13. Da Ãdãwa da Fir`auna da `yan`uwan Lũɗu.
-
14. Da ma`abũta ƙunci da mutãnen Tubba`u, kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata.
-
15. Shin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? Ã`a, su sunã a cikin rikici daga halitta sãbuwa.
-
16. Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar jannayẽnsa.
-
17. A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani (malã`ika) zaunanne.
-
18. Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce.
-
19. Kuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirẽwa.
-
20. Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa.
-
21. Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida.
-
22. (Sai a ce masa): "Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne."
-
23. Kuma abõkin haɗinsa ya ce: "Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce."
-
24. (A ce wa Malã`iku), "Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai tsaurin rai."
-
25. "Mai yawan hanãwa ga alhẽri, mai zãlunci, mai shakka."
-
26. "Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa shi a cikin azãba mai tsanani."
-
27. Abõkin haɗinsa ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa."
-
28. Ya ce: "Kada ku yi husũma a wuriNa, alhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku."
-
29. "Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyiNa."
-
30. Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe, akwai wani ƙãri?"
-
31. Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba.
-
32. "Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa`adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa).
-
33. "Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali."
-
34. (A ce musu) "Ku shige ta da aminci, waccan ita ce rãnar dawwama."
-
35. Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni`ima,
-
36. Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al`ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa`an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: `Kõ akwai wurin tsĩra`? (Babu).
-
37. Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa).
-
38. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata`yar wahala ba ta shãfe Mu ba.
-
39. Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta.
-
40. Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada.
-
41. Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri makusanci.
-
42. Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari).
-
43. Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take.
-
44. Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu.
-
45. Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur`ani, ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa.
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas