An-Naba - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. A kan mẽ suke tambayar jũna?
-
2. A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur`ãni)?
-
3. Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?
-
4. A`aha! Zã su sani.
-
5. Kuma, a`aha! Zã su sani.
-
6. Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?
-
7. Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?
-
8. Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?
-
9. Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?
-
10. Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?
-
11. Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci?
-
12. Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?
-
13. Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?
-
14. Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?
-
15. Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?
-
16. Da itãcen lambuna mãsu lillibniya?
-
17. Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci.
-
18. Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama`a jama`a.
-
19. Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi.
-
20. Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.
-
21. Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata.
-
22. Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma.
-
23. Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna.
-
24. Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha.
-
25. Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini.
-
26. Sakamako mai dãcẽwa.
-
27. Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi.
-
28. Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyinMu, ƙaryatãwa!
-
29. Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce.
-
30. Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba.
-
31. Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.
-
32. Lambuna da inabõbi.
-
33. Da cikakkun `yammata, tsãrar jũna.
-
34. Da hinjãlan giya cikakku.
-
35. Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.
-
36. Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.
-
37. Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.
-
38. Rãnar da Rũhi da malã`iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.
-
39. Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.
-
40. Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!"
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas