Ad-Dukhan - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. Ḥ. M̃.
-
2. Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani.
-
3. Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ` Mun kasance Mãsu yin gargaɗi.
-
4. A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne.
-
5. Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã.
-
6. Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani.
-
7. (Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka).
-
8. Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.
-
9. A`a sũ, sunã wãsã a cikin shakka.
-
10. Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne.
-
11. Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi.
-
12. Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne.
-
13. Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)?
-
14. Sa`an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci."
-
15. Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin).
-
16. Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne.
-
17. Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir`auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu.
-
18. (Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku."
-
19. "Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne."
-
20. "Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni."
-
21. "Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni."
-
22. Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi.
-
23. (Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)"
-
24. "Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa."
-
25. Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari.
-
26. Da shuke-shuke da matsayi mai kyau.
-
27. Da wata ni`ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu.
-
28. Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam.
-
29. Sa`an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.
-
30. Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã`ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa.
-
31. Daga Fir`auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna.
-
32. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne.
-
33. Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu`ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni`ima bayyananna
-
34. Lalle waɗannan mutãne, haƙĩka, sunã cẽwa,
-
35. "Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."
-
36. "Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."
-
37. shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba`u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi.
-
38. Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã.
-
39. Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.
-
40. Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa`adinsu gabã ɗaya.
-
41. Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba.
-
42. fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
-
43. Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã),
-
44. Ita ce abincin mai laifi.
-
45. Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna.
-
46. Kamar tafasar ruwan zãfi.
-
47. (A cẽ wa malã`ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa`an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm."
-
48. "Sa`an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi."
-
49. (A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!"
-
50. "Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi."
-
51. Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce.
-
52. A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari.
-
53. Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna.
-
54. Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu.
-
55. Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan `ya`yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro).
-
56. Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm.
-
57. Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.
-
58. Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur`ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa.
-
59. Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne.
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas