logo HARUN YAHYA

Al-Infitar - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Idan sama ta tsãge.
  • 2. Kuma idan taurãri suka wãtse.
  • 3. Kuma idan tẽkuna aka facce su.
  • 4. Kuma idan kaburbura aka tõne su.
  • 5. Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.
  • 6. Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.
  • 7. Wanda Ya halitta ka sa`an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.
  • 8. A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.
  • 9. A`aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!
  • 10. Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.
  • 11. Mãsu daraja, marubũta.
  • 12. Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.
  • 13. Lalle ne, mãsu ɗã`ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni`ima.
  • 14. Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.
  • 15. Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.
  • 16. Bã zã su faku daga gare ta ba.
  • 17. Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako?
  • 18. Sa`an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?
  • 19. Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al`amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code