Al-Qalam - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa.
-
2. Kai, sabõda ni`imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba.
-
3. Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa.
-
4. Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya.
-
5. Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani.
-
6. Ga wanenku haukã take.
-
7. Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkinSa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.
-
8. Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa.
-
9. Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta.
-
10. Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce.
-
11. Mai zunɗe, mai yãwo da gulma.
-
12. Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi.
-
13. Mai girman kai, bãyan haka kuma la`ĩmi (bã ya son alhẽri).
-
14. Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya.
-
15. Idan ana karanta masa ãyõyinMu, sai ya ce: "Tatsũniyõyin mutãnen farko ne."
-
16. Zã Mu yi masa alãma a kan hanci.
-
17. Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci.
-
18. Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa.
-
19. Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, (ya ƙone ta,) alhãli sunã barci.
-
20. Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare.
-
21. Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci.
-
22. Cẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa.
-
23. Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cẽwa).
-
24. "Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau!"
-
25. Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu.
-
26. Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: "Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)!"
-
27. "Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne."
-
28. Mafificinsu (hankali) ya ce: "Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah?"
-
29. Suka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai."
-
30. Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu.
-
31. Suka ce: "Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka."
-
32. "Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne."
-
33. Haka dai azãbar take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnẽwã.
-
34. Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni`ima.
-
35. Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa`a kamar mãsu laifi?
-
36. Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka)?
-
37. Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa?
-
38. Cẽwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa?
-
39. Kõ kunã (riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kanMu, har ya zuwa Rãnar ¡iyãma, cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku?
-
40. Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin)?
-
41. Kõ sunã da abõkan tãrẽwa (ga wannan ra`ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya.
-
42. Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujũda, sai bã zã su iyãwa ba.
-
43. Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi).
-
44. Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur`ãni). Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba.
-
45. Ina jinkirtã musu, lalle kaidiNa mai ƙarfi ne.
-
46. Kõ kana tambayar su wata la`ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu?
-
47. Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga gare shi) ne?
-
48. Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma`abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi.
-
49. Ba dõmin ni`ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi.
-
50. Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa`an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki.
-
51. Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur`ãni, kuma sunã cẽwa, "Lalle ne shi mahaukaci ne!"
-
52. Shi (Alƙur`ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya.
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas