logo HARUN YAHYA

Ash-Shams - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta.
  • 2. Kuma da wata idan ya bi ta.
  • 3. Da yini a lõkacin da ya bayyana ta.
  • 4. Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta.
  • 5. Da sama da abin da ya gina ta.
  • 6. Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.
  • 7. Da rai da abin da ya daidaita shi.
  • 8. Sa`an nan ya sanar da shi fãjircinsa da shiryuwarsa.
  • 9. Lalle ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya sãmi babban rabo.
  • 10. Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe shi (da laifi) ya tãɓe.
  • 11. Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.
  • 12. A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).
  • 13. Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!"
  • 14. Sai suka ƙaryata shi, sa`an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa`an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).
  • 15. Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code