logo HARUN YAHYA

Adh-Dhariyat - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa.
  • 2. Sa`an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa).
  • 3. Sa`an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi.
  • 4. Sa`an nan da Malã`iku mãsu rabon al`amari (bisa umurnin Allah).
  • 5. Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne.
  • 6. Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne
  • 7. Inã rantsuwa da samã ma`abũciyar hanyõyi (na tafiyar taurãri da sautin rediyo).
  • 8. Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur`ani).
  • 9. Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya).
  • 10. An la`ani mãsu ƙiri-faɗi.
  • 11. Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci.
  • 12. Sunã tambaya: "Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku?"
  • 13. Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su.
  • 14. (A ce musu): "Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa."
  • 15. Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari.
  • 16. Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã su. Lalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya).
  • 17. Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci.
  • 18. Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri.
  • 19. Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo.
  • 20. Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni.
  • 21. Kuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi). To, bã zã ku dũbã ba?
  • 22. Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari.
  • 23. To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana,
  • 24. Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka?
  • 25. A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce "Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi!"
  • 26. Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa`an nan ya zo da maraƙi tutturna,
  • 27. Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: "Bã zã ku ci ba?"
  • 28. Sai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro." Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi.
  • 29. Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: "Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)!"
  • 30. Suka ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi."
  • 31. (Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al`almarinku, yã kũ Manzanni!"
  • 32. Suka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi.
  • 33. "Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom).
  • 34. "Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna."
  • 35. Sa`an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai.
  • 36. Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi.
  • 37. Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi.
  • 38. Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir`auna da wani dalĩli bayyananne.
  • 39. Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci!"
  • 40. Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa`an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
  • 41. Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu.
  • 42. Bã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa.
  • 43. Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci,"
  • 44. Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo.
  • 45. Ba su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba.
  • 46. Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.
  • 47. Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa.
  • 48. Kuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ,
  • 49. Kuma daga kõme Mun halitta nau`i biyu, watakila zã ku yi tunãni.
  • 50. Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.
  • 51. Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.
  • 52. Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci."
  • 53. shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã`a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai.
  • 54. Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne.
  • 55. Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai.
  • 56. Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini.
  • 57. Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni.
  • 58. Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.
  • 59. To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa.
  • 60. Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari.
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code