logo HARUN YAHYA

Al-Buruj - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara.
  • 2. Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,
  • 3. Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta a cikinsa
  • 4. An la`ani mutãnen rãmi.
  • 5. Wato wuta wadda aka hura.
  • 6. A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune.
  • 7. Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce.
  • 8. Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa.
  • 9. Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake.
  • 10. Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa`an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara.
  • 11. Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba.
  • 12. Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai.
  • 13. Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa).
  • 14. Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya.
  • 15. Mai Al`arshi mai girma
  • 16. Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi.
  • 17. Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka.
  • 18. Fir`auna da samũdãwa?
  • 19. Ã`aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa.
  • 20. Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da saninSa).
  • 21. Ã`aha! Shi Alƙur`ãni ne mai girma.
  • 22. A cikin Allo tsararre.
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code