Al-Mujadila - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. Lalle Alla Ya ji maganar wadda ke yi maka jãyayya game da mijinta, tanã kai ƙãra ga Allah, kuma Allah nã jin muhawararku. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani.
-
2. Waɗanda ke yin zihãri daga cikinku game da mãtansu, sũmãtan nan bã uwãyensu ba ne, bãbu uwayensu fãce waɗanda suka haife su. Lalle sũ, sunã faɗar abin ƙyãmã na magana da ƙarya, kuma lalle Allah haƙĩƙa Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara.
-
3. Waɗanda ke yin zihãri game da mãtansu, sa`an nan su kõma wa abin da suka faɗa, to, akwai `yanta wuya a gabãnin su shãfi jũna. Wannan anã yi muku wa`azi da shi. Kuma Allah Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatãwa.
-
4. To, wanda bai sãmu ba, sai azumin wata biyu jẽre a gabãnin su shãfi jũna, sa`an nan wanda bai sãmi ĩkon yi ba, to, sai ciyar da miskĩnai sittin. Wannan dõmin ku yĩ ĩmãni da Allah da Manzonsa. Kuma waɗannan hukunce-hukunce haddõdin Allah ne. Kuma kãfirai, sunã da azãba mai raɗadi.
-
5. Lalle waɗanda ke sãɓã wa Allah da ManzonSa, an wulãkanta su kamar yadda aka wulãkantar da waɗanda ke a gabãninsu, kuma lalle Mun saukar da ãyõyi bayyanannu, kuma kãfirai nã da azãba mai wulãkantãwa.
-
6. Rãnar da Allah zai tãyar da su gabã ɗaya, sa`an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka aikata, Allah Yã lissafa shi, alhãli kuwa sũ, sun manta da shi, kuma a kan kõme Allah Halartacce ne.
-
7. Ashe, ba ka ga cẽwa lalle Allah Yanã sane da abin da yake a cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa ba? Wata gãnãwa ta mutum uku bã zã ta kasance ba fãce Allah Shĩ ne na huɗu ɗinta, kuma bãbu ta mutum biyar fãce Shĩ ne na shida ɗinta, kuma babu abin da ya kãsa wannan kuma babu abin da yake mafi yawa fãce Shĩ Yanã tãre da su duk inda suka kasance, sa`an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka aikata a Rãnar ¡iyãma. Lalle Allah Masani ne ga dukkan kõme.
-
8. Ashe, ba ka ga waɗanda aka hane su ba daga ganãwar, sa`an nan sunã kõmã wa abin da aka hane su daga gare shi, kuma sunã gãnãwa game da zunubi da zãlunci da sãɓã wa Manzon Allah, kuma idan sun zo maka sai su gasihe ka da abin da Allah bai gaishe ka da shi ba, kuma sunã cẽwa a cikin zukatansu: "Don me Allah ba Ya yi mana azãba sabõda abin da muke faɗi?" Jahannama ita ce mai isarsu, zã su shigeta. Sabõda haka makõmarsu ta mũnana.
-
9. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan za ku yi gãnãwa, to, kada ku gãna game da zunubi da zãlunci da sãɓã wa Manzon Allah, kuma ku yi gãnãwa game da alhẽri da taƙawa. Ku bi Allah da taƙawa wanda zã a tattara ku zuwa gare, shi.
-
10. Gãnãwar daga Shaiɗan take kawai dõmin ya mũnanã wa waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli kuwa bã zai iya cũtar su da kõme ba fãce da iznin Allah. Kuma sai mũminai su dogara ga Allah.
-
11. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan an ce muka, "Ku yalwatã a cikin majalisai," to, ku yalwatã, sai Allah Ya yalwatã muku, kuma idan an ce muku, "Ku tãshi" to, ku tãshi. Allah nã ɗaukaka waɗanda suka yi ĩmãni daga cikinku da waɗanda aka bai wa ilim wasu darajõji mãsu yawa, kuma, Allah Mai ƙididdigewa ne ga dukan kõme.
-
12. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan zã ku gãnãwa da Manzon Allah, to, ku gabãtar da `yar sadaka a gabãnin gãnãwarku, wannan ne mafi alhẽri a gare ku, kuma mafi tsarki. Sai idan ba ku sãmi (abin sadakar ba), to, lalle, Allah, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
-
13. Ashe, kun ji tsõron ku gabãtar da sadakõki a gabãnin gãnãwarku? To, idan ba ku aikata ba, kuma Allah Ya kõmo da ku zuwa ga sauƙi, sai ku tsai da salla, kuma ku bãyar da zakka, kuma ku yi ɗã`ã ga Allah da ManzonSa. Kuma Allah ne Mai ƙididdigewa ga abin da kuke aikatãwa.
-
14. Ashe, baka ga waɗanda suka jiɓinci waɗansu mutãne da Allah Ya yi hushi a kansu ba, bã su cikinku, kuma bã su a cikinsu kuma sunã rantsuwa a kan ƙarya, alhãli kuwa sunã sane?
-
15. Allah Ya yi musu tattalin azãba mai tsanani. Lalle sũ abin da suka kasance sunã aikatãwa ya mũnana.
-
16. Sun riƙi rantsuwõwinsu garkuwa, sabõda haka suka kange (mũminai) daga jihãdin ɗaukaka tafarkin Allah. To, sunã da azãba mai wulãkantãwa.
-
17. Dũkiyõyinsu ba su wadãtar musu kõme ba daga Allah, haka kuma ɗiyansu. Waɗannan `yan wutã ne. Sũ, mãsu dawwama ne a cikinta.
-
18. Rãnar da Allah ke tãyar da su gabã ɗaya, sai su yi Masa rantsuwa kamar yadda suke yi muku rantsuwa (a nan dũniya) kuma sunã zaton cẽwa sũ a kan wani abu suke! To, lalle sũ, sũ ne maƙaryata.
-
19. Shaiɗan ya rinjaya a kansu, sai ya mantar da su ambaton Allah, waɗannan ƙungiyar Shaiɗan ne. To, lalle ƙungiyar Shaiɗan, sũ ne mãsu hasãra.
-
20. Lalle, waɗanda ke sãɓã wa Allah da ManzonSa waɗannan sunã a cikin (mutãne) mafi ƙasƙanci.
-
21. Allah Ya rubũta cẽwa," Lalle zan rinjãya, Nĩ da ManzanniNa." Lalle Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi.
-
22. Bã zã ka sãmi mutãne mãsu yin ĩmãni da Allah da RãnarLãhira sunã sõyayya da wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa ba, kõ dã sun kasance ubanninsu ne, kõ ɗiyansu kõ `yan`uwansu, ko danginsu. waɗannan Allah Yã rubuta ĩmãni a cikin zukãtansu, kuma Yã ƙarfafa su da wani rũhi daga gare Shi, kuma zai shigar da su a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Allah Yã yarda da su, kuma sun yarda da Shi. Waɗannan ƙungiyar Allah ne. To, lalle ƙungiyar Allah sũ ne mãsu babban rabo.
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas