Al-Mutaffifin - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.
-
2. Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.
-
3. Kuma idan sun auna musu da zakka ko da sikẽli, suna ragẽwa
-
4. Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?
-
5. Domin yini mai girma.
-
6. Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?
-
7. Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.
-
8. Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?
-
9. Wani 1ittãfi ne rubũtacce.
-
10. Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
-
11. Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.
-
12. Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.
-
13. Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.
-
14. A`aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.
-
15. A`aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.
-
16. Sa`an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.
-
17. Sa`an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi."
-
18. A`aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã`ã yana a cikin Illiyyĩna?
-
19. Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?
-
20. Wani littãfi ne rubũtacce.
-
21. Muƙarrabai suke halarta shi.
-
22. Lalle ne, mãsu ɗã`ã ga Allah tabbas suna cikin ni`ima.
-
23. A kan karagu, suna ta kallo.
-
24. Kana sani a cikin huskõkinsu, akwai kwarjinin ni`ima.
-
25. Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.
-
26. ¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma.
-
27. Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.
-
28. (Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.
-
29. Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.
-
30. Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.
-
31. Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.
-
32. Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne."
-
33. Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.
-
34. To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya.
-
35. A kan karagu, suna ta kallo.
-
36. Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas