Nuh - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu.
-
2. Ya ce: "Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa."
-
3. "Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõronSa, kuma ku bĩ ni."
-
4. "Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci)."
-
5. Nũhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini."
-
6. "To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni)."
-
7. "Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai."
-
8. "Sa`an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane."
-
9. "Sa`an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri."
-
10. "Shi na ce, `Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne."
-
11. "Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga."
-
12. "Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna."
-
13. "Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah,"
-
14. "Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye?"
-
15. "Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba?"
-
16. "Ya sanya watã a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rãnã babbar fitila?"
-
17. "Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa (kamar ganye) tsirarwa."
-
18. "Sa`an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa."
-
19. "Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya."
-
20. "Dõmin ku shiga a cikinta, hanyõyi mãsu fãɗi."
-
21. Nũhu ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne sũ sun saɓa mini sun bi wanda dukiyarsa da ɗiyansa ba su ƙãre shi da kõme ba sai da hasãra."
-
22. "Kuma sun yi wani mãkirci, mãkirci babba."
-
23. "Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumãkanku, kuma faufau, kada ku bar wadda, kuma kada ku bar suwã kuma kada ku bar Yagũsa da Ya`ũƙa da Nasra."
-
24. "Kuma lalle ne sun ɓatar da (mutãne) mãsu yawa, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai (kõme) sai ɓata."
-
25. Sabõda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa`an nan aka sanya su a wuta. Saboda haka ba su sãmã wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba.
-
26. Kuma Nũhu ya ce: "Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai, wanda ke zama a cikin gida."
-
27. "Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyinKa, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci"
-
28. "Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai kõme sai halaka."
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas