21. Al-Anbya - Alqur'ani
- 1. Hisãbin mutãne ya kusanta gare su, ahãli kuwa sunã a cikin gafala, sunã mãsu bijirẽwa.
- 2. Wani ambatõ daga Ubangijinsu sãbo, bã ya zuwa gare su fãce sun saurãre shi, alhãli kuwa sunã mãsu yin wãsa.
- 3. Sanã mãsu shagaltacin zukãtansu, kuma su asirta gãnãwa: Waɗanda suka yi zãlunce (sunã cẽwa) "Wannan bã Kõwa ba ne fãce mutum misãlinku. Shin, to, kunã jẽ wa sihiri, ahãli kuwa kũ, kunã fahimta?"
- 4. Ya ce: "Ubangijina Yanã sanin magana a cikin sama da ƙasa kuma Shi ne Mai ji, Masani."
- 5. Ã`a, suka ce: "Yãye-yãyen mafarki ne. Ã`a, yã ƙirƙira shi ne. Ã`a, shi mawãƙi ne. Sai ya zo mana da wata ãyã kamar yadda aka aiko manzanni na farko."
- 6. Wata alƙarya da Muka halaka ta a gabãninsu, ba ta yi ĩmãni ba. Shin, to, sũ, sunã yin ĩmãni?
- 7. Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã yin wahayi zuwa gare su. Ku tambayi ma`abũta ambato idan kun kasance ba ku sani ba.
- 8. Kuma ba Mu sanya su jiki, bã su cin abin ci ba, kuma ba su kasance madawwama ba.
