logo HARUN YAHYA

Abasa - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Yã game huska kuma ya jũya bãya.
  • 2. Sabõda makãho yã je masa.
  • 3. To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka.
  • 4. Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi?
  • 5. Amma wanda ya wadãtu da dũkiya.
  • 6. Sa`an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi!
  • 7. To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba?
  • 8. Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa.
  • 9. Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah.
  • 10. Kai kuma kã shagala ga barinsa!
  • 11. A`aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce.
  • 12. Sabõda wanda ya so ya tunaShi (Allah).
  • 13. (Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa,
  • 14. Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa.
  • 15. A cikin hannãyen mala`iku marubũta.
  • 16. Mãsu daraja, mãsu ɗã`a ga Allah.
  • 17. An la`ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa!
  • 18. Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?
  • 19. Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa`an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye).
  • 20. Sa`an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa.
  • 21. Sa`an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.
  • 22. Sa`an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi.
  • 23. Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari).
  • 24. To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa.
  • 25. Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa.
  • 26. Sa`an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa.
  • 27. Sa`an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta.
  • 28. Da inabi da ciyãwa.
  • 29. Da zaitũni da itãcen dabĩno.
  • 30. Da lambuna, mãsu yawan itãce.
  • 31. Da `yã`yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi.
  • 32. Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku.
  • 33. To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo.
  • 34. Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan`uwansa.
  • 35. Da uwarsa da ubansa.
  • 36. Da mãtarsa da ɗiyansa.
  • 37. Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha`ani da ya ishe shi.
  • 38. Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne.
  • 39. Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra.
  • 40. Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu.
  • 41. Baƙi zai rufe su.
  • 42. Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu).
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code