logo HARUN YAHYA

Az-Zalzalah - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta.
  • 2. Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi.
  • 3. Kuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta?"
  • 4. A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta.
  • 5. cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta.
  • 6. A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu.
  • 7. To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi.
  • 8. Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi.
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code