logo HARUN YAHYA

Al-`Adiyat - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.
  • 2. Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.
  • 3. Sa`an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.
  • 4. Sai su motsar da ƙũra game da shi.
  • 5. Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama`ar maƙiya.
  • 6. Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.
  • 7. Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka.
  • 8. Kuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.
  • 9. Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.
  • 10. Aka bayyana abin da ke cikin zukata.
  • 11. Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code