23. Al-Mu`minun - Alqur'ani
- 1. Lalle ne, Mũminai sun sãmi babban rabõ.
- 2. Waɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli`u ne.
- 3. Kuma waɗanda suke, sũdaga barin yasassar magana, mãsu kau da kai ne.
- 4. Kuma waɗanda suke ga zakka mãsu aikatãwa ne.
- 5. Kuma waɗanda suke ga farjõjinsu mãsu tsarẽwa ne.
- 6. Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka to lalle sũ bã waɗanda ake zargi, ba, ne.
- 7. Sabõda haka wanda ya nẽmi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙẽtarẽwar haddi.
- 8. Kuma waɗanda suke, sũga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
- 9. Kuma da waɗanda suke, sũ a kan sallõlinsu sunã tsarẽwa.
