97. Al-Qadr - Alqur'ani
- 1. Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi (Alƙur`ãni) a cikin Lailatul ƙadari (daren daraja)
- 2. To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul ¡adari?
- 3. Lailatul ¡adari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu.
- 4. Mala`iku da Rũhi suna sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu sabõda kowane umurni.
- 5. Sallama ne shi daren, har fitar alfijiri.
