11. Hud - Alqur'ani
- 1. A. L̃.R. Littãfi ne an kyautata ãyõyinsa, sa`an nan an bayyanã su daki-daki, daga wurin Mai hikima, Mai ƙididdigewa.
- 2. Kada ku bautã wa kõwa fãce Allah. Lalle ne ni a gare ku mai gargaɗi ne kuma mai bushãrã daga gare Shi.
- 3. Kuma ku nẽmi gãfara gun Ubangijinku. Sa`an nan ku tũba zuwa gare Shi, Ya jiyar da ku dãɗi, jiyarwa mai kyau zuwa ga ajali ambatacce, kuma Ya bai wa dukkan ma`abucin, girma girmansa. Amma idan kun jũya, to, lalle nĩ, inã tsõron azãbar yini mai girma a kanku.
- 4. Zuwa ga Allah makõmarku take, kuma Shĩ a kan kõmeMai ĩkon yi ne.
- 5. To, lalle sũ sunã karkatar da ƙirjinsu dõmin su ɓõye daga gare shi. To, a lõkacin da suke lulluɓẽwa da tufãfinsu Yanã sanin abin da suke ɓoyewa da abin da suke bayyanãwa. Lalle Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãzã.
- 6. Kuma bãbu wata dabba a cikin ƙasa fãce ga Allah arzikinta yake, kuma Yanã sanin matabbatarta da ma`azarta, duka sunã cikin littãfi bayyananne.
- 7. Kuma shi ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwanaki shida, kuma Al`arshinSa ya kasance akan ruwa, dõmin Ya jarrabã ku, wannan ne daga cikinku mafi kyãwon aiki. Kuma haƙĩƙa idan ka ce: "Lalle kũ waɗanda ake tãyarwa ne a bãyan mutuwa," haƙĩƙa waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Wannan bai zama ba fãce sihiri bayyananne."
