Al-Mumtahanah - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku riƙi maƙiyĩNa kuma maƙiyinku masõyi, 845. Kuna jẽfa sõyayya zuwa gare su, alhãli kuwa haƙĩƙa sun kãfirta da abin da ya zo muku, na gaskiya, sunã fitar da Manzon Allah tãre da ku (daga gidãjenku) dõmin kun yi ĩmãni da Allah, Ubangijinku, idan kun fito dõmin jihãdi sabõda ɗaukaka kalmaTa da nẽman yardaTa, kunã asirta sõyayya zuwa gare su alhãli kuwa Nĩ ne Mafi sani ga abin da kuka ɓõye da abin da kuka bayyana, kuma duk wanda ya aikata shi daga cikinku, to, lalle ya ɓace daga tsakar hanya.
-
2. Idan sun kãma ku, zã su kasance maƙiya a gare ku, kuma su shimfiɗa hannuwansu da harsunan gũrin ku kãfirta.
-
3. Zumuntarku bã zã ta amfãne ku ba, haka kuma ɗiyanku, a Rãnar Kiyãma. (Allah) zai rarrabe tsakãninku, kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.
-
4. Lalle abin kõyi mai kyau ya kasance a gare ku game da Ibrãhĩm da waɗanda ke tãre da shi a lõkacin da suka ce wa mutnensu, "Lalle mũ bãbu ruwanmu daku, kuma da abin da kuke bautãwa, baicin Allah, mun fita batunku, kuma ƙiyayya da jiyẽwa jũna sun bayyana a tsakãninmu, sai kun yi ĩmãni da Allah Shi kaɗai." Fãce maganar Ibrãhĩm ga ubansa (da yace), "Lalle za ni nẽma maka gãfara kuma ban mallaki kõme ba daga Allah sabõda kai." "Yã Ubangijinmu! A gare Ka muka dõgara, kuma gare Ka muka mayar da al` amuranmu, kuma zuwa gare Ka makõma take."
-
5. "Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu fitina ga waɗanda suka kãfirta, kuma Ka yi gãfara gare Mu. Ya Ubangijinmu! Kai ne Mabuwãyi, Mai hikima!
-
6. Lalle, haƙĩƙa, abin kõyi mai kyau ya kasance a gare ku daga cikinsu, ga wanda ya kasance yanã fãtan (rahamar) Allah da Rãnar Lãhira, kuma wanda ya jũya bãya, to, lalle Allah, Shĩ ne wadãtacce, Gõdadde.
-
7. Anã tsammãnin Allah Ya sanya, a tsakãninku da tsakãnin waɗanda kuka yi ƙiyayya da su, wata sõyaya daga gare su, kuma Allah Mai ĩkon yi ne, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
-
8. Allah bã Ya hana ku, daga waɗanda ba su yãƙe ku ba sabõda addini kuma ba su fitar da ku ba daga gidãjenku, ga ku kyautata musu kuma ku yi musu ãdalci. Lalle Allah Yanã son mãsu ãdalci.
-
9. Allah Yanã hana ku kawai daga waɗanda suka yãke ku sabõda addini kuma suka fitar da ku daga gidãjenku, kuma suka taimaki jũna ga fitar da ku, karku jiɓince su, kuma wanda ya jiɓince su, to waɗannan sũ ne azzãlumai.
-
10. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan mãtã mũminai suka zo muku, sunã mãsu hijira, to, ku jarraba su. Allah Shĩ ne mafi sani ga ĩmãninsu. To, idan kun san sũ mũminai ne, kada ku mayar da su zuwa ga kãfirai. Sũ mãtan bã su halatta ga aurensu, sũ kuma kãfiran bã su halatta ga auren mãtan. Ku bã su abin da suka ɓatar na dũkiya. Kuma bãbu laifi a kanku ga ku aure su idan kun bã su sadãkõkinsu. Kuma kada ku riƙe auren mãtã kãfirai, kuma ku tambayi abin da kuka ɓatar daga dũkiya, su kuma kãfirai su tambayi abin da suka ɓatar na dũkiya. Wannan hukuncin Allah ne Yanã hukunci a tsakãninku. kuma Allah, Masani ne, Mai hikima
-
11. Kuma idan wani abu ya kuɓuce muku daga mãtanku zuwa ga kãfirai sa`an nan kuma kuka ɗauki fansa, to, sai ku bai wa waɗanda matansu suka tafi kwatankwacin abin da suka ɓatar na dũkiya. Kuma ku yi biyayya da taƙawa ga Allah wanda kuke mãsu ĩmãni da Shi, Shi Kaɗai.
-
12. Yã kai Annabi! Idan mãtã mũminai suka zo maka sunã yi maka mubãya`a a kan bã zã su yi shirki da Allah ba ga kõme, kuma bã su yin sãtã, kuma bã su yin zina, kuma bã su kashe, ya`yansu, kuma bã su zuwa da ƙarya da suke ƙirƙirãwa a tsãkanin hannuwansu da ƙafãfunsu kuma bã su sãɓa maka ga wani abu da aka sani na sharĩ`a, to, ka karɓi mubãya`arsu, kuma ka nẽmi Allah Ya gãfarta musu. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
-
13. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku jiɓinci waɗansu mutãne da Allah Ya yi hushi a kansu. Lalle sun yanke tsammãni daga (rahamar) Lãhira, kamar yadda kãfirai suka yanke tsammãni daga mazõwa kaburbura.
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas