logo HARUN YAHYA

Al-Layl - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa.
  • 2. Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa.
  • 3. Da abin da ya halitta namiji da mace.
  • 4. Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke.
  • 5. To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa.
  • 6. Kuma ya gaskata kalma mai kyãwo.
  • 7. To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.
  • 8. Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa.
  • 9. Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.
  • 10. To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani.
  • 11. Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta).
  • 12. Lãlle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya.
  • 13. Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne.
  • 14. Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka.
  • 15. Bãbu mai shigarta sai mafi shaƙãwa.
  • 16. Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya.
  • 17. Kuma mafi taƙawa zai nisance ta.
  • 18. Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka.
  • 19. Alhãli bãbu wani mai wata ni`ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta.
  • 20. Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka.
  • 21. To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi).
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code