As-Saffat - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).
-
2. Sa`an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi.
-
3. Sa`an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.
-
4. Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne.
-
5. Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.
-
6. Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.
-
7. Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.
-
8. Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama`a mafi ɗaukaka (Malã`iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe.
-
9. Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.
-
10. Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.
-
11. Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.
-
12. Ã`a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.
-
13. Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.
-
14. Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.
-
15. Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne."
-
16. "Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?
-
17. "Ashe kõ da ubanninmu na farko?"
-
18. Ka ce: "Na`am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu."
-
19. Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.
-
20. Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako."
-
21. Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa.
-
22. Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa.
-
23. Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm.
-
24. Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.
-
25. Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?
-
26. Ã`a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne.
-
27. Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna.
-
28. Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)."
-
29. Suka ce: "Ã`a, ba ku kasance mũminai ba.
-
30. "Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã`a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka."
-
31. "Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne."
-
32. "Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu."
-
33. To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar.
-
34. Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.
-
35. Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai.
-
36. Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?
-
37. Ã`a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni.
-
38. Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.
-
39. Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
-
40. Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
-
41. Waɗannan sunã da abinci sananne.
-
42. `Ya`yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.
-
43. A cikin gidãjen Aljannar ni`ima.
-
44. A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna.
-
45. Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari.
-
46. Farã mai dãɗi ga mashãyan.
-
47. A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,
-
48. Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.
-
49. Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye.
-
50. Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna.
-
51. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)."
-
52. Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?"
-
53. "Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?"
-
54. (Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?"
-
55. Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim.
-
56. Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni."
-
57. "Kuma bã dõmin ni`imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)."
-
58. "Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba."
-
59. "Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?"
-
60. Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma.
-
61. Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa.
-
62. Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm?
-
63. Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai.
-
64. Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm.
-
65. Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne.
-
66. To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa`an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta.
-
67. Sa`an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi.
-
68. Sa`an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take.
-
69. Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu.
-
70. Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa.
-
71. Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu.
-
72. Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu.
-
73. Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.
-
74. Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
-
75. Kuma lalle, haƙĩƙa` Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu.
-
76. Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba.
-
77. Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa.
-
78. Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama`ar ƙarshe.
-
79. Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu.
-
80. Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
-
81. Lalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai.
-
82. Sã`an nan Muka nutsar da waɗansunsu.
-
83. Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.
-
84. A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya.
-
85. A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?"
-
86. "Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?"
-
87. "To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?"
-
88. Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri.
-
89. Sã`an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne."
-
90. Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya.
-
91. Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa`an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba?
-
92. "Me ya sãme ku, bã ku magana?"
-
93. Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma.
-
94. Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa.
-
95. Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa,
-
96. "Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?"
-
97. Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa`an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm."
-
98. Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci.
-
99. Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni."
-
100. "Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne."
-
101. Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri.
-
102. To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri."
-
103. To, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga gẽfen gõshinsa.
-
104. Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!"
-
105. "Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
-
106. Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.
-
107. Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.
-
108. Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.
-
109. Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.
-
110. Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
-
111. Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.
-
112. Kuma Muka yi masa bushãra Da Is`hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.
-
113. Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is`hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin).
-
114. Kuma lalle, Mun yi ni`ima ga Mũsã da Hãrũna.
-
115. Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma.
-
116. Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya.
-
117. Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni.
-
118. Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya.
-
119. Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe.
-
120. Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna.
-
121. Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
-
122. Lalle, sunã daga bãyinMu mũminai.
-
123. Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
-
124. A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?"
-
125. "Shin, kunã bauta wa Ba`al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?"
-
126. "Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?"
-
127. Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã).
-
128. Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
-
129. Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe.
-
130. Aminci ya tabbata ga Ilyãs.
-
131. Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
-
132. Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.
-
133. Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
-
134. A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya.
-
135. Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba).
-
136. Sã`an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen.
-
137. Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci.
-
138. Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba?
-
139. Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.
-
140. A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi.
-
141. Sã`an nan ya yi ƙuri`a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.
-
142. Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.
-
143. To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,
-
144. Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.
-
145. Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.
-
146. Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi.
-
147. Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka).
-
148. Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.
-
149. Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da `ya`ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?"
-
150. Kõ kuma Mun halitta malã`iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce?
-
151. To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa.
-
152. "Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne.
-
153. Shin, Yã zãɓi `yã`ya mãtã ne a kan ɗiya maza?
-
154. Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannanhukunci)?
-
155. Shin, bã ku tunãni?
-
156. Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne?
-
157. To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya.
-
158. Kuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)"
-
159. Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa.
-
160. Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
-
161. To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa,
-
162. Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi.
-
163. Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm.
-
164. "Kuma bãbu kõwa daga cikinmu, fãce yanã da matsayi sananne."
-
165. "Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)."
-
166. "Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi."
-
167. Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa,
-
168. "Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko."
-
169. "Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."
-
170. Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani.
-
171. Kuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni.
-
172. Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako.
-
173. Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya.
-
174. Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci.
-
175. Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani.
-
176. Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa?
-
177. To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana.
-
178. Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci.
-
179. Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa.
-
180. Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa.
-
181. Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni.
-
182. Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas