105. Al-Fil - Alqur'ani
- 1. Ashe, ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa ba?
- 2. Ashe, bai sanya kaidinsu a cikin ɓata ba?
- 3. Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama`a-jama`a.
- 4. Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta.
- 5. Sa`an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?
