At-Talaq - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. Ya kai Annabi! Idan kun saki mãtã, sai ku sake su ga iddarsu, kuma ku ƙididdige iddar. Kuma ku bi Allah Ubangijinku da taƙawa. Kada ku fitar da su daga gidãjensu, kuma kada su fita fãce idan sunã zuwa da wata alfãshã bayyananna. Kuma waɗancan iyakõkin Allah ne. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to, lalle ya zãlunci kansa. Ba ka sani ba ɗammãnin Allah zai fitar da wani al`amari a bãyan haka.
-
2. Sa`an nan idan sun isa ga ajalinsu (na idda) sai ku riƙe su da abin da aka sani kõ ku rabu da su da abin da aka sani kuma ku shaidar da mãsu adalci biyu daga gare ku. Kuma ku tsayar da shaidar dõmin Allah. Wancan ɗinku anã yin wa`azi da shi ga wanda ya kasance yanã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai sanya masa mafita.
-
3. Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato. Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, Allah ne Ma`ishinsa. Lalle Allah Mai iyar da umurninSa ne. Haƙĩƙa Allah Ya sanyama`auni ga dukan kõme.
-
4. Kuma waɗanda suka yanke ɗammãni daga haila daga mãtanku, idan kun yi shakka, to, iddarsu watã uku ce da waɗanda ba su yi haila ba. Kuma ma`abũta cikinna ajalinsu, (shi ne) cewa su haifi cikinnansu. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, (Allah) zai sanya masa wani sauƙi daga al`amarinsa.
-
5. Wancan umurnin Allah ne, Ya saukar da shi zuwa gare ku. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai kankare masa mũnãnan ayyukansa, kuma Ya girmama masa sãkamako.
-
6. Ku zaunar da su daga inda kuka zaunar daga gwargwadon sãmunku. Kuma kada ku cũce su dõmin ku ƙuntata a kansu. Kuma idan sun kasance ma`abũta ciki, sai ku ciyar da su har su haifi cikinsu. Sa`an nan idan sun shãyar da mãma sabõda ku, sai ku bã su tsãdõdinsu. Kuma ku yi shãwara a tsakãninku bisa abin da aka sani. Kuma idan kun nũna talauci to wata mace zã ta shãyar da mãma sabõda shi (mijin).
-
7. Sai mawadãci ya ciyar daga wadãtarsa kuma wanda aka ƙuntata masa arzikinsa, to, sai ya ciyar daga abin da Allah Ya bã shi. Allah bã Ya kallafa wa wani rai fãce abin da Ya bã shi. Allah zai sanya sauƙi a bãyan tsanani.
-
8. Kuma da yawa daga alƙarya wadda ta yi tsaurin kai daga barin umurnin Ubangijinta da ManzanninSa, sai Muka yi mata hisãbi, hisãbi mai tsanani, kuma Muka, azabtar da ita azãba abar ƙyãma.
-
9. Sa`an nan ta ɗanɗana masĩfar al`amarinta. kuma ƙarshen al`amarinta ya kasance hasãra,
-
10. Allah Ya yi musu tattalin wata azãba mai tsanani. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, yã ma`abũta hankula, waɗanda suka yi ĩmãni! Haƙĩƙa Allah Ya saukar da wata tunãtarwa zuwa gare ku.
-
11. Manzo, yanã karãtun ãyõyin Allah bayyananu a kanku dõmin Ya fitar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai daga duffai zuwa ga haske. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah ya aikata aikin ƙwarai Allah zai shigar da shi gidãjen Aljanna ƙoramu nã gudãna daga ƙarƙashnsu sunã mãsu dawwama a cikinsu har abada. Haƙĩƙa Allah Yã kyautata masa arziki.
-
12. Allah, wanda Ya halitta bakwai ɗin sammai kuma daga ƙasã kwatankwacinsu, umuruinSa yanã ta sauka a tsakaninsu dõmin ku san lalle Allah Mai ĩkon yi ne akan dukan kõme, kuma lalle Allah, haƙĩƙa Ya kẽwaye ga dukan kõme da sani.
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas