38. Sad - Alqur'ani
- 1. Ṣ̃, Inã rantsuwa da Al-ƙur`ãni mai hukunce-hukunce.
- 2. Ã`a, waɗanda suka kãfirta sunã cikin girman kai (ga rikon al`ãdunsu) da sãɓãni (tsakãnin jũnansu).
- 3. Da yawa Muka halakar da wani ƙarni, a gabãninsu, suka yi kira (nẽman cẽto), bãbu lõkacin kuɓucewa.
- 4. Kuma suka yi mãmãki dõmin Mai gargaɗi, daga cikinsu, ya je musu. Kuma kãfirai sukace, "Wannan mai sihiri ne, maƙaryaci."
- 5. "Shin, yã sanya gumãka duka su zama abin bautawa guda? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmaki!"
- 6. Shũgabanni daga cikinsu, suka tafi (suka ce),"Ku yi tafiyarku, ku yi haƙuri a kan abũbuwan bautawarku. Lalle wannan, haƙiƙa, wani abu ne ake nufi!"
- 7. "Ba mu taɓa ji ba, game da wannan a cikin addinin ƙarshe. Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya."
- 8. "Shin, an saukar da Alƙur`ãni ne a kansa, a tsakãninmu (mũ kuma ba mu gani ba)?" Ã`a, su dai sunã cikin shakka daga hukunciNa Ã`a, ba su i da ɗanɗanar azãba ba.
