logo HARUN YAHYA

Al-Qamar - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Sã`a ta yi kusa, kuma wata ya tsãge.
  • 2. Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!"
  • 3. Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al`amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.
  • 4. Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.
  • 5. Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.
  • 6. Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama.
  • 7. ¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse.
  • 8. Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya!"
  • 9. Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata BawanMu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi.
  • 10. Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako."
  • 11. Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba.
  • 12. Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umurni da aka riga aka ƙaddara shi.
  • 13. Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi.
  • 14. Tanã gudãna, a kan idãnunMu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin.
  • 15. Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni
  • 16. To, yãyã azãbãTa take da gargaɗiNa?
  • 17. Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur`ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
  • 18. Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗiNa?
  • 19. Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa.
  • 20. Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne.
  • 21. To, yãya azãbãTa take da gargaɗiNa?
  • 22. Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur`ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
  • 23. Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin.
  • 24. Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã.
  • 25. "Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã`a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai!"
  • 26. Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan?
  • 27. Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri.
  • 28. Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa.
  • 29. Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa`an nan ya sõke ta,
  • 30. To, yãya azãbaTa take da gargaɗiNa?
  • 31. Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge.
  • 32. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur`ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
  • 33. Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi.
  • 34. Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba.
  • 35. Sabõda wata ni`ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde.
  • 36. Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙarMu, sai suka yi musu game da gargaɗin.
  • 37. Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. "To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩNa."
  • 38. Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe.
  • 39. To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩNa.
  • 40. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
  • 41. Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir`auna.
  • 42. Sun ƙaryata game da ãyõyinMu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi.
  • 43. Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã`a a cikin littattafai?
  • 44. Kõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?"
  • 45. Zã a karya tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu.
  • 46. Ã`a, Sã`a ita cẽ lõkacin wa`adinsu, kuma Sã`ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci.
  • 47. Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka.
  • 48. Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar."
  • 49. Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri.
  • 50. Kuma umurninMu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido.
  • 51. Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?
  • 52. Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai.
  • 53. Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne.
  • 54. Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna.
  • 55. A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa.
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code