logo HARUN YAHYA

Ash-Sharh - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)?
  • 2. Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe.
  • 3. Wanda ya nauyayi bãyanka?
  • 4. Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka?
  • 5. To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
  • 6. Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
  • 7. Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah).
  • 8. Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi.
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code