logo HARUN YAHYA

Al-Fatihah - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
  • 2. Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;
  • 3. Mai rahama, Mai jin ƙai;
  • 4. Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.
  • 5. Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa.
  • 6. Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.
  • 7. Hanyar waɗanda Ka yi wa ni`ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code