An-Nazi`at - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. Ina rantsuwa da mala`iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.
-
2. Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.
-
3. Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.
-
4. Sa`an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsẽre.
-
5. Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni.
-
6. Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.
-
7. Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.
-
8. Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.
-
9. Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.
-
10. Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?
-
11. "Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?"
-
12. Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!"
-
13. To, ita kam, tsãwa guda kawai ce.
-
14. Sai kawai gã su a bãyan ƙasa.
-
15. Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?
-
16. A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?
-
17. Ka tafi zuwa ga Fir`auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi.
-
18. "Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka.
-
19. "Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?"
-
20. Sai ya nũna masa ãyar nan mafi girma.
-
21. Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni),
-
22. Sa`an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri.
-
23. Sai ya yi gayya, sa`an nan ya yi kira.
-
24. Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka."
-
25. Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko.
-
26. Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah.
-
27. Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.
-
28. Ya ɗaukaka rufinta, sa`an nan Ya daidaita ta.
-
29. Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.
-
30. Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta.
-
31. Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta.
-
32. Da duwatsu, Yã kafe ta.
-
33. Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku.
-
34. To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo.
-
35. Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata.
-
36. Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani.
-
37. To, amma wanda ya yi girman kai.
-
38. Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya).
-
39. To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma.
-
40. Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.
-
41. To, lalle ne Aljanna ita ce makõma.
-
42. Sunã tambayar ka game da sa`a, wai yaushe ne matabbatarta?
-
43. Me ya haɗã ka da ambatonta?
-
44. Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al`amarinta yake.
-
45. Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta.
-
46. Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa.
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas