logo HARUN YAHYA

Al-Qari`ah - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!
  • 2. Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?
  • 3. Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?
  • 4. Rãnar da mutãne za su kasance kamar `ya`yan fari mãsu wãtsuwa.
  • 5. Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe.
  • 6. To, amma wanda ma`aunansa suka yi nauyi.
  • 7. To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.
  • 8. Kuma amma wanda ma`aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi).
  • 9. To, uwarsa Hãwiya ce.
  • 10. Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?
  • 11. Wata wuta ce mai zafi.
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code