Al-Waqi`ah - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. Idan mai aukuwa ta auku.
-
2. Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.
-
3. (Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.
-
4. Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.
-
5. Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.
-
6. Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.
-
7. Kuma kun kasance nau`i uku.
-
8. Watau mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
-
9. Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?
-
10. Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,
-
11. Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.
-
12. A ckin Aljannar ni`ima.
-
13. Jama`a ne daga mutãnen farko.
-
14. Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.
-
15. (Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu.
-
16. Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.
-
17. Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.
-
18. Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.
-
19. Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.
-
20. Da wasu `ya`yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.
-
21. Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha`awa.
-
22. Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.
-
23. Kamar misãlan lu`ulu`u wanda aka ɓõye.
-
24. A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.
-
25. Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.
-
26. Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun.
-
27. Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
-
28. (Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.
-
29. Da wata ayaba mai yawan `ya`ya.
-
30. Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya.
-
31. Da wani ruwa mai gudãna.
-
32. Da wasu `ya`yan itacen marmari mãsu yawa.
-
33. Bã su yankẽwa kuma bã a hana su.
-
34. Da wasu shimfiɗu maɗaukaka.
-
35. Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.
-
36. Sa`an nan Muka sanya su budurwai.
-
37. Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.
-
38. Ga mazõwa dãma.
-
39. Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko.
-
40. Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.
-
41. Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?
-
42. Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.
-
43. Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.
-
44. Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni`ima ba.
-
45. Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.
-
46. Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma.
-
47. Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?"
-
48. "Shin, kuma da ubanninmu na farko?"
-
49. Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe."
-
50. "Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne."
-
51. "Sa`an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!"
-
52. "Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)."
-
53. "Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta."
-
54. "Sa`an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi."
-
55. "Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa."
-
56. Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.
-
57. Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?
-
58. Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?
-
59. Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?
-
60. Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa ba,
-
61. A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.
-
62. Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?
-
63. Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?
-
64. Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?
-
65. Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.
-
66. (Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!"
-
67. "Ã`a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!"
-
68. Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?
-
69. Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?
-
70. Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?
-
71. Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?
-
72. Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?
-
73. Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa`azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.
-
74. Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.
-
75. To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.
-
76. Kuma lalle ne` haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.
-
77. Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.
-
78. A cikin wani littafi tsararre.
-
79. Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.
-
80. Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.
-
81. Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?
-
82. Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?
-
83. To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).
-
84. Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.
-
85. Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.
-
86. To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?
-
87. Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.
-
88. To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,
-
89. Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni`ima.
-
90. Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,
-
91. Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.
-
92. Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,
-
93. Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.
-
94. Da ƙõnuwa da Jahĩm,
-
95. Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.
-
96. Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangijinka, Mai karimci.
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas