Al-Haqqah - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. Kiran gaskiya!
-
2. Mẽne ne kiran gaskiya?
-
3. Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya?
-
4. Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya!
-
5. To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani.
-
6. Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi.
-
7. (Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi.
-
8. To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu?
-
9. Kuma Fir`auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi.
-
10. Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani).
-
11. Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan.
-
12. Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi).
-
13. To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya.
-
14. Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya.
-
15. A ran nan, mai aukuwa zã ta auku.
-
16. Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce.
-
17. Kuma malã`iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã`iku) takwas na ɗauke da Al`arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar.
-
18. A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa.
-
19. To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina."
-
20. "Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne."
-
21. Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda.
-
22. A cikin Aljanna maɗaukakiya.
-
23. Nunannun `yã`yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba),
-
24. (Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni`ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige."
-
25. Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba!"
-
26. "Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba!"
-
27. "In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce!
-
28. "Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba!"
-
29. "Ĩkona ya ɓace mini!"
-
30. (Sai a ce wa malã`iku) "Ku kãmã shi, sa`an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi."
-
31. "Sa`an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi."
-
32. "Sa`an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã`i saba`in, sai ku sanya shi."
-
33. "Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma!"
-
34. "Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci!"
-
35. "Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi."
-
36. "Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn."
-
37. "Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci."
-
38. To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba,
-
39. Da abin da bã ku iya gani.
-
40. Lalle ne, shi (Alƙur`ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne.
-
41. Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata.
-
42. Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa.
-
43. Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka.
-
44. Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu.
-
45. Dã Mun kãma shi da dãma.
-
46. sa`an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã.
-
47. Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbarMu) daga gare shi.
-
48. Kuma lalle ne shi (Alƙur`ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa.
-
49. Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa.
-
50. Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai.
-
51. Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙshẽni.
-
52. Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma.
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas