logo HARUN YAHYA

Al-`Alaq - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.
  • 2. Ya hahitta mutum daga gudan jini.
  • 3. Ka yi karatu, kuma UbangiJinka shi ne Mafi karimci.
  • 4. Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami.
  • 5. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.
  • 6. A`aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu).
  • 7. Dõmin yã ga kansa, yã wadãta.
  • 8. Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.
  • 9. Shin, kã ga wanda ke hana.
  • 10. Bãwã idan yã yi salla?
  • 11. Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?
  • 12. Ko ya yi umurni da taƙawa?
  • 13. Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?
  • 14. Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?
  • 15. A`aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa.
  • 16. Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi.
  • 17. Sai ya kirayi ƙungiyarsa.
  • 18. Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala`iku mãsu girma).
  • 19. A`aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali`u, kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code