Al-Jinn - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. Ka ce: "An yi wahayi zuwa gare ni cewa wasu jama`a na aljannu sun saurũri (karatuna), sai suka ce: Lalle ne mũ mun ji wani abin karantãwa (Alƙui`ãni), mai ban mãmãki."
-
2. "Yana nũni zuwa ga hanyar ƙwarai, sabõda haka mun yi ĩmãni da shi bã zã mu kõma bautã wa Ubangijinmu tãre da kõwa ba."
-
3. "Kuma lalle ne shĩ girman Ubangijinmu, Ya ɗaukaka, bai riƙi mãta ba, kuma bai riƙi ɗã ba."
-
4. "Kuma lalle ne shi, wãwanmu ya kasance yana faɗar abin da ya ƙetare haddi ga Allah."
-
5. "Kuma lalle ne mũ, mun yi zaton mutum da aljani bã zã su iya faɗar ƙarya ba ga Allah."
-
6. "Kuma lalle ne shi wasu maza daga cikin mutãne, sun kasance sunã nẽman tsari da wasu maza daga cikin aljannu, sabõda haka suka ƙara musu girman kai."
-
7. "Kuma lalle ne sũ, sun yi zato, kamar yadda kuka yi zato, cewa Allah bã zai aiko kowa ba."
-
8. "Kuma lalle ne mũ mun nẽmi (hawan) sama, sai muka, sãme ta an cika ta da tsaro mai tsanani da kuma yũlãye."
-
9. "Kuma lalle ne mũ, mun kasance muna zama daga garẽta, a wurãren zama dõmin saurare. To wanda ya yi saurãre a yanzu, zai sãmi yũla, mai dãko dõminsa."
-
10. "Kuma lalle ne mũ ba mu sani ba, shin, sharri ne aka yi nufi ga waɗanda ke cikin ƙasa, ko Ubangijinsu Yã yi nufin shiriya a gare su ne?"
-
11. "Kuma lalle ne mũ, akwai sãlaihai a cikinmu, kuma akwai a cikinmu waɗanda ba haka bã mun kasance ƙungiyõyi dabam-dabam."
-
12. "Kuma lalle ne mũ mun tabbatã bã zã mu buwãyi Allah ba, a cikin ƙasa, kuma bã zã mu buwãye Shi da gudu ba."
-
13. "Kuma lalle ne mũ, a lõkacin da muka ji shiriya, mun yi ĩmãni da ita. To wanda ya yi ĩimãni da Uhangijinsa, bã zai ji tsõron nakkasa ba, kuma bã zai ji tsõron zãlunci ba."
-
14. "Kuma lalle ne mũ akwai a cikinmu, waɗanda suka mĩƙa wuya, kuma akwai a cikinmu karkatattu. to, wanda ya mĩƙa wuya waɗancan kam sun nufi shiryuwa."
-
15. "Kuma amma karkatattu sai suka kasance makãmashi ga Jahannama."
-
16. "Kuma dã sun tsayu sõsai a kan hanya, dã lalle Mun shãyar da su ruwa mai yawa."
-
17. "Domin Mu jarraba su a ciki, kuma wanda ya kau da kai daga tuna Ubangijinsa, Ubangijinsa zai shigar da shi azãba mai hauhawa."
-
18. "Kuma lalle ne wurãren sujada na Allah ne, saboda haka kada ku kira kõwa tãre da Allah (da su, a cikinsu)."
-
19. "Kuma, lalle ne shi, a lõkacin da bãwan Allah ke kiran Sa sun yi kusa su zama kamar shirgi a kansa."
-
20. Ka ce: "lna kiran Ubangijina ne kawai, kuma bã zan tãra kowa da Shi ba."
-
21. Ka ce: "Lalle ne, nĩ bã ni mallakar wata cũta gare ku, kuma bã ni mallakar wani alhẽri."
-
22. Ka ce: "Lalle ne, nĩ kõwa bã ya iya cẽtona daga Allah, kuma bã zan iya sãmun mafaka ba daga gare Shi."
-
23. "Fãce iyarwa, daga Allah, da manzancinsa. To, wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, to, lalle yana da wutar Jahannama suna mãsu dawwama a cikinta, har abada."
-
24. Har idan sun ga abin da ake yi musu gargaɗi da shi, to, zã su san wanda ya zama mafi raunin mataimaki da mafi ƙarancin adadi.
-
25. Ka ce: "Ban sani ba a kusa ne abin da ake yi muku gargaɗi da shi, ko Ubangijina Ya sanya maSa dõgon ajali!"
-
26. "Shi ɗai ne Masanin fake sabõda haka, bã Ya bayyana gaibinSa ga kowa."
-
27. "Fãce ga wanda Yã yarda da shi, wato wani manzo sa`an nan lalle ne, zai sanya gãdi a gaba gare shi da bãya gare shi."
-
28. "Dõmin Ya san lalle, sun iyar da sãƙonnin Ubangijinsu, kuma (Shi Ubangijin) Yã kẽwaye su da sani, kuma Yã lissafe dukan kõme da ƙididdiga."
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas