logo HARUN YAHYA

Ar-Rahman - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. (Allah) Mai rahama.
  • 2. Yã sanar da Alƙur`ani.
  • 3. Yã halitta mutum.
  • 4. Yã sanar da shi bayãni (magana).
  • 5. Rãnã da watã a kan lissãfi suke.
  • 6. Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu`i.
  • 7. Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli.
  • 8. Dõmin kada ku karkatar da sikẽlin.
  • 9. Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin.
  • 10. Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai.
  • 11. A cikinta akwai `ya`yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa.
  • 12. Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi.
  • 13. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangjinku kuke ƙaryatãwa?
  • 14. Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko.
  • 15. Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã.
  • 16. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 17. Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã.
  • 18. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 19. Yã garwaya tẽku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa.
  • 20. A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba.
  • 21. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 22. Lu`ulu`u da murjãni na fita daga gare su.
  • 23. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 24. Kuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tẽku kamar manyan duwãtsu.
  • 25. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 26. Dukkan wanda ke kanta mai ƙãrẽwa ne.
  • 27. Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa.
  • 28. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 29. wanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha`ani.
  • 30. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 31. Zã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ mãsu nauyin halitta biyu!
  • 32. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 33. Ya jama`ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcẽwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcẽwaba fãce da wani dalĩli.
  • 34. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 35. Anã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nẽmi taimako ba?
  • 36. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 37. Sa`an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta.
  • 38. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 39. To, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani.
  • 40. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 41. zã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu.
  • 42. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 43. Wannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita.
  • 44. Sunã kẽwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa.
  • 45. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 46. Kuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu.
  • 47. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 48. Mãsu rassan itãce.
  • 49. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 50. A cikinsu akwai marẽmari biyu sunã gudãna.
  • 51. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 52. A cikinsu akwai nau`i biyu daga kõwane `ya`yan itãcen marmari.
  • 53. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 54. Sunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun `yã`yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke.
  • 55. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 56. A cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani.
  • 57. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 58. Kamar dai su yaƙũtu ne da murjãni.
  • 59. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 60. Shin, kyautatãwa nã da wani sakamako? (Ã`aha) fãce kyautatãwa.
  • 61. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 62. Kuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu.
  • 63. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 64. Mãsu duhun inuwa.
  • 65. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 66. A cikinsu akwai marẽmari biyu masu kwarãrar ruwa.
  • 67. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 68. A cikinsu akwai `ya`yan itãcen marmari da dabĩno darummãni.
  • 69. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 70. A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyaun hãlãye, mãsu kyaun halitta.
  • 71. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 72. Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi.
  • 73. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 74. Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani.
  • 75. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 76. Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa.
  • 77. To, sabõda wanne daga ni`imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
  • 78. Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka.
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code