Al-Muzzammil - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. Yã wanda ya lulluɓe!
-
2. Ka tsayu domin yin salla a cikin dare (duka) fãce kaɗan.
-
3. Rabinsa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi.
-
4. Ko ka ƙara kansa kuma ka kyautata karanta Alƙu`ãni, daki daki.
-
5. Lalle ne, Mũ, zã Mu jẽfa maka magana mai nauyi.
-
6. Lalle ne, tashin dare shi ne mafi tsananin natsuwa, kuma mafi daidaituwa ga magana.
-
7. Lalle ne, kanã da, a cikin yini, wani tasĩhi mai tsawo.
-
8. Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, kuma ka yanke (ƙauna daga kowa ka koma) zuwa gare Shi, yankewa.
-
9. Shi ne Ubangijin mafitar rãnã da mafãɗarta, bãbu abin bautawa fãce Shi. Sabõda haka ka riƙe Shi wakili.
-
10. Kuma ka yi haƙuri ga abin da suke faɗã, kuma ka ƙaurace musu, ƙauracẽwa mai kyãwo.
-
11. Kuma ka bar Ni da mãsu ƙaryatãwa, mawadãta, kuma ka jinkirta musu kaɗan.
-
12. Lalle ne, a wurinMu, akwai wasu marũruwa mãsu nauyi da Jahĩm.
-
13. Da wani abinci mai mãƙara da azãba mai raɗaɗi.
-
14. Rãnar da ƙasa ke raurawa, da duwãtsu kuma duwãtsu su kasance tudun rairayi mai malãlã.
-
15. Lalle ne, Mũ. Mun aika zuwa gare ku, wani Manzo mai shaida a kanku, kamar yadda Muka aika wani Manzo zuwaga Fir`auna,
-
16. Sai Fir`auna ya saɓa wa Manzon, saboda haka Muka kãma shi kãmu mai tsanani.
-
17. To, yãya, idan kun kãfirta, zã ku kãre (azabar) wani yini mai mayar da yãra (tsofaffi) mãsu hurhura.
-
18. Sama za ta tsãge a cikinsa, wa`adinsa yã kasance mai aukuwa.
-
19. Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, sai dai wanda ya so, ya kãma hanyar ƙwarai zuwa ga Ubangijinsa.
-
20. Lalle ne, Ubangijinka Yã sani cẽwa, kai kana tsayuwa a kusan kashi biyu daga uku na dare, da rabinsa, da sulusinsa, tãre da wani ɓangare na waɗanda ke tãre da kai. Allah Yake iya ƙaddara dare da yini, Ya san bã zã ku iya lissafa shi ba, sabõda haka Ya karɓi tubarku sai, ku karanta abin da ya sauƙaƙa na Alƙur`ãni. Ya san wasu daga cikinku, zã su yi cĩwo, kuma wasu zã su yi tafiya cikin ƙasa suna nẽman falalar Allah da fatauci, kuma wasu zã su yi yãƙi a cikin banyar Allah. Sabõda haka ku karanta abin da ya sauƙaƙa daga gare shi, kuma ku tsai da salla kuma ku bãyar da zakka, kumaa ku bai wa Allah rance, rance mai kyãwo. Kuma abin da kuka gabatar dõmin kanku, na alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah zai kasance mafifici (daga wanda kuka ajiye) kuma zai fi girma ga sakamako, kuma ku rõƙi Allah gãfara; lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas