logo HARUN YAHYA

Al-Mursalat - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.
  • 2. Sa`an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.
  • 3. Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.
  • 4. sa`an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.
  • 5. Sa`an nan da malã`iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.
  • 6. Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.
  • 7. Lalle ne, abin da ake yi muku wa`adi da shi tabbas mai aukuwa ne
  • 8. To, idan taurãri aka shãfe haskensu.
  • 9. Kuma, idan sama aka tsãge ta.
  • 10. Kuma, idan duwãtsu aka nike su.
  • 11. Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.
  • 12. Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.
  • 13. Domin rãnar rarrabẽwa.
  • 14. Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?
  • 15. Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
  • 16. Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.
  • 17. Sa`an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?
  • 18. Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.
  • 19. Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
  • 20. Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.
  • 21. Sa`an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.
  • 22. Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.
  • 23. Sa`an nan, Muka nũna iyãwarMu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa.
  • 24. Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
  • 25. Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba.
  • 26. Ga rãyayyu da matattu,
  • 27. Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?
  • 28. Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
  • 29. Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!
  • 30. Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.
  • 31. Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta.
  • 32. Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye.
  • 33. Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe.
  • 34. Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
  • 35. Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba.
  • 36. Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari.
  • 37. Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
  • 38. Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko.
  • 39. To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.
  • 40. Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
  • 41. Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari.
  • 42. Da wasu `ya`yan itãce irin waɗanda suke marmari.
  • 43. (A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni`ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."
  • 44. Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
  • 45. Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
  • 46. (Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne."
  • 47. Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
  • 48. Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ`i; bã zã su yi rukũ`in (salla) ba."
  • 49. Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
  • 50. To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur`ãni) zã su yi ĩmãni
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code