logo HARUN YAHYA

Al-A`la - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.
  • 2. Wanda Yã yi halitta sa`an nan Ya daidaita abin halittar.
  • 3. Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri).
  • 4. Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.
  • 5. Sa`an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.
  • 6. Za mu karantar da kai (Alƙur`ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.
  • 7. Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye.
  • 8. Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al`amari) zuwa ga (Shari`a) mai sauƙi.
  • 9. Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.
  • 10. Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna.
  • 11. Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta,
  • 12. Wanda zai shiga wutar da tã fi girma.
  • 13. Sa`an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.
  • 14. Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.
  • 15. Kuma ya ambaci sũnan Ubangijinsa, sa`an nan yã yi salla.
  • 16. Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.
  • 17. Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.
  • 18. Lalle ne, wannan yanã a cikin littafan farko.
  • 19. Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã.
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code