logo HARUN YAHYA

At-Tin - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.
  • 2. Da Dũr Sĩnĩna.
  • 3. Da wannan gari amintacce.
  • 4. Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.
  • 5. Sa`an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
  • 6. Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.
  • 7. To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?
  • 8. Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code