Al-Insan - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. Lalle ne, wata mudda ta zamani tã zo a kan mutum, bai kasance kõme ba wanda ake ambata.
-
2. Lalle ne, Mũ Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi, sabõda haka Muka sanya shi mai ji mai gani,
-
3. Lalle ne, Mũ, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai gõdiya, kuma ko ya zama mai kãfirci.
-
4. Lalle ne, Mũ, Mun yi tattali, dõmin kãfirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa`ĩr.
-
5. Lalle ne, mutãnen kirki zã su sha daga finjãlin giya abin gaurayarta yã kãsance kãfur ne.
-
6. Wani marmaro ne, daga gare shi bayin Allah suke sha, suna ɓuɓɓugar da shi ɓuɓɓugarwa.
-
7. Suna cikãwa da alwãshin (da suka bãkanta), kuma suna tsõron wani yini wanda sharrinsa ya kasance mai tartsatsi ne.
-
8. Kuma suna ciyar da abinci, a kan suna bukãtarsa, ga matalauci da marãya da kãmamme.
-
9. (Suna cẽwa): "Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya.
-
10. "Lalle ne, mũ muna tsõro daga Ubangijinmu, wani yini mai gintsẽwa, mai murtukẽwa."
-
11. Sabõda haka Allah Ya tsare musu sharrin wannan yini, kuma Ya hlɗa su da annũrin huska da farin ciki,
-
12. Kuma Ya sãka musu sabõda haƙurin da suka yi, da Aljanna da tufãfin alharini.
-
13. Sunã mãsu zaman ginciri, a cikinta, a kan karagu, bã su ganin rãnã a cikinta, kuma bã su ganin jaura.
-
14. Kuma, inuwõyinta suna kusa, a kansu, an hõre nunannun `yã`yan itãcenta, hõrẽwa.
-
15. Kuma ana kẽwayãwa a kansu da finjãlai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance na ƙarau.
-
16. ¡arau na azurfa, sun ƙaddara su ƙaddarawa, daidai bukãta.
-
17. Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance zanjabil ne.
-
18. Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil.
-
19. Kuma wasu yara samãrin dindindin na kẽwayãwa, a kansu, idan ka gan su, zã ka zaci sũ lu`ulu`u ne wanda aka wãtsa.
-
20. Kuma idan kã ga wannan wurin, to, kã ga wata irin ni`ima da mulki babba.
-
21. Tufãfinsu na sama na alharĩ ni ne, kõre da mai walƙiya, kuma an ƙawãce su da mundãye na wata curin azurfa kuma Ubangijinsu, Ya shãyar da su abin sha mai tsarkakẽwar (ciki).
-
22. (A ce musu) "Lalle ne, wannan ya kasance, a gare ku sakamako, kuma aikink. ya kasance abin gõdewa."
-
23. Lalle, Mũ ne Muka saukar da Alƙur`ãni a gare ka, saukarwa.
-
24. Sabõda haka ka yi haƙuri ga hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi, daga cikinsu, mai zunubi ko mai kãfirci.
-
25. Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, sãfe da maraice.
-
26. Daga dare, sai ka yi sujũda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi darẽ mai tsawo.
-
27. Lalle ne, waɗannan suna son mai gaugãwa (dũniya) kuma suna bari, a bãyansu, wani yini mai nauyi.
-
28. Mũ ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu musanyâ su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa.
-
29. Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa ga Ubangijinsa.
-
30. Kuma, bã zã ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Yã kasance Masani` Mai hikima.
-
31. Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzãlumai, Yã yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi.
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas