93. Ad-Duhaa - Alqur'ani
- 1. Inã rantsuwa da hantsi.
- 2. Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).
- 3. Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.
- 4. Kuma lalle ta ƙarshe ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
- 5. Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.
- 6. Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa`an nan Ya yi maka makõma?
- 7. Kuma Ya sãme ka bã ka da shari`ã, sai Ya shiryar da kai?
- 8. Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?
- 9. Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.
