114. An-Nas - Alqur'ani
- 1. Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne."
- 2. "Mamallakin mutane."
- 3. "Abin bautãwar mutãne."
- 4. "Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa."
- 5. "Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane."
- 6. "Daga aljannu da mutane."
