Al-Mulk - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. (Allah), Wanda gudãnar da mulki yake ga hannunSa, Ya tsarkaka, kuma Shi Mai ĩko ne a kan kome.
-
2. Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba ku, Ya nũna wãye daga cikinku ya fi kyãwon aiki, Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara.
-
3. Shi ne wanda Ya halitta sammai bakawi, ɗabaƙõƙi a kan jũna, bã za ka ga goggociya ba a cikin halittar (Allah) Mai rahama. Ka sãke dũbawa, ko za ka ga wata ɓaraka?
-
4. Sa`an nan ka sake maimaita, dũbãwa, ganinka zai komo maka, gajiyayye, ba da ganin wata naƙasa bã.
-
5. Kuma lalle Mun ƙawãta samar farko da fitillu, kuma Muka sanya su abin jifa ga shaiɗanu, kuma Muka yi musu tattalin azãbar Sa`ĩr.
-
6. Kuma waɗanda suka kafirce wa Ubangjinsu na da azãbar Jahannama, tã munana ga zamanta makõmarsu.
-
7. Idan an jẽfa su a cikinta, sai su ji daga gare ta wata ƙãra, tana tafasa.
-
8. Tana kusa ta tsãge domin hushi, ko da yaushe aka jẽfa wani ɓangaren jama`a a cikinta, matsaranta na tambayar su da cewa, "Wani mai gargaɗi bai je muku ba?"
-
9. Sai su ce: "I, lalle wani mai gargaɗi ya je mana, sai muka ƙaryata shi, muka ce, `Allah bai saukar da kome ba, bã ku cikin kõme sai ɓata babba.`"
-
10. Kuma suka ce: "Dã mun zamo muna saurãre, kõ muna da hankali, dã ba mu kasance a cikin `yan sa`ĩr ba."
-
11. Wato su yi iƙrãri da laifinsu. Allah Ya la`ani`yan sa`ĩr!
-
12. Lalle waɗanda ke tsõron Ubangjinsu, a ɓoye, suna da wata gãfara da wani sakamako mai girma.
-
13. Kuma ku asirta maganarku ko ku bayyana ta, lalle shi, (Allah), Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza.
-
14. Ashe, wanda Ya yi halitta bã zai iya saninta ba, alhãli kuwa shi Mai tausasãwa ne, kuma Mai labartawa?
-
15. Shi, (Allah), Yã sanya muku ƙasa hõrarriya, sai ku tafi cikin sãsanninta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma zuwa gare shi ne tãshin yake.
-
16. Shin kõ kun amince cewa wanda ke cikin sama, bã zai iya shãfe ƙasa tãre da ku ba, sai ga ta tana mai girgiza?
-
17. Kõ kun amincẽ cewa wanda ke cikin sama bã zai iya sako muku iskar gũguwa ba? To, zã ku san yadda (ãƙibar) gargaɗiNa take.
-
18. Lalle, waɗanda ke gabansu sun ƙaryata (manzanni). To, yãya (ãƙibar) gargaɗiNa ta kasance?
-
19. Bã zã su yi dũbi ba zuwa ga tsuntsãye a kansu, mãsu sanwã, kuma suna fiffikãwa, bãbu mai riƙe da su sai (Allah), Mairahama? Lalle shi Mai gani ne ga dukan kõme.
-
20. Wãne ne wanda zai zame muku mayãƙin da zai taimake ku, wanda bã (Allah) ba, Mai rahama? Kãfirai ba su a cikin kõme fãce rũɗu.
-
21. Wãne ne wanda zai ciyar da ku, idan (Allah) Ya riƙe arzikinSa? A`aha, sun yi zurfi cikin girman kai da tãshin hankali.
-
22. Shin, wanda ke tafiya a kife a kan fuskarsa yã fi zama a kan shiryuwa, ko kuwa wanda ke tafiya miƙe a kan hanya madaidaiciya?
-
23. Ka ce: "(Allah) Shine Wanda Ya ƙaga halittarku, Ya sanya muku ji da gani da tunãni, amman kaɗan ce ƙwarai godiyarku!"
-
24. Kuma kace "Shi ne Ya halitta ku daga ƙasã, kuma zuwa gareShi ne ake tãshin ku."
-
25. Kuma sunã cewa, "Yaushe ne wannan alkawarin zai tabbata in dai kun kasance mãsu gaskiya ne kũ?"
-
26. Ka ce: "Ilmin a wurin Allah kawai yake, kuma ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyana (gargaɗin)."
-
27. To, lokacin da suka gan ta (azãbar) a kusa, fuskokin waɗanda suka kãfirta suka mũnana, kuma aka ce (musu) wannan shi ne abin da kuka zamo kuna ƙaryatãwa.
-
28. Ka ce musu "Idan Allah Ya halaka ni nĩ da wanda ke tãre da ni, ko kuma, Yã yi mana rahama, to, wãne ne zai tserar da kafirai daga wata azãba mai raɗaɗi?"
-
29. Ka ce: "Shĩ ne Mai rahama mun yi ĩmãni da Shi, gare Shi muka dogara, saboda haka zã ku san wanda yake a cikin ɓata bayyananniya."
-
30. Ka ce: "Ko kun gani, idan ruwanku ya wãyi gari faƙaƙƙe, to, wãne ne zai zo muku da ruwa wani mai ɓuɓɓuga?"
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas