logo HARUN YAHYA

Al-Qiyamah - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Bã sai Nã yi rantsuwa da Rãnar ¡iyãma ba.
  • 2. Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin kansa ba.
  • 3. Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?
  • 4. Na`am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.
  • 5. Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.
  • 6. Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?"
  • 7. To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).
  • 8. Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).
  • 9. Aka tãra rãnã da watã
  • 10. Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?"
  • 11. A`aha! bãbu mafaka.
  • 12. zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.
  • 13. Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.
  • 14. Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.
  • 15. Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).
  • 16. Kada ka mõtsar da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur`ãni).
  • 17. Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.
  • 18. To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.
  • 19. sa`an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.
  • 20. A`aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.
  • 21. Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira).
  • 22. Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.
  • 23. Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.
  • 24. Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.
  • 25. Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.
  • 26. A`aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.
  • 27. kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?"
  • 28. Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.
  • 29. Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.
  • 30. Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa take.
  • 31. To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!
  • 32. Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!
  • 33. Sa`an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.
  • 34. Halaka tã tabbata a gare ka, sa`an nan ita ce mafi dãcewa.
  • 35. Sa`an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.
  • 36. Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?
  • 37. Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)
  • 38. Sa`an nan, ya zama gudan jini, sa`an nan Allah Ya halitta shi, sa`an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;
  • 39. Sa`an nan, Ya sanya daga gare shi, nau`i biyu: namiji damace?
  • 40. Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code