logo HARUN YAHYA

Al-Humazah - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa).
  • 2. Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa.
  • 3. Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi.
  • 4. A`aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama.
  • 5. Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama?
  • 6. Wutar Allah ce wadda ake hurawa.
  • 7. Wadda take lẽƙãwa a kan zukata.
  • 8. Lalle ne ita abar kullẽwa cea kansu.
  • 9. A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu.
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code