111. Al-Masad - Alqur'ani
- 1. Hannãye biyu na Abũlahabi sun halaka, kuma ya halaka.
- 2. Dũkiyarsa ba ta tsare masa kõme ba, da abin da ya tãra.
- 3. Zã ya shiga wuta mai hũruwa.
- 4. Tãre da matarsa mai ɗaukar itacen (wuta).
- 5. A cikin kyakkyãwan wuyanta akwai igiya ta kaba (Rãnar ¡iyãma).
