28. Al-Qasas - Alqur'ani
- 1. ¦. S̃. M̃.
- 2. Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.
- 3. Munã karantãwa a kanka daga lãbarin Mũsã da Fir`auna da gaskiya dõmin mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.
- 4. Lalle ne Fir`auna ya ɗaukaka a cikin ƙasa, kuma ya sanya mutãnenta ƙungiya-ƙungiya, yanã raunanar da wata jama`a daga gare su; yanã yanyanka ɗiyansu maza kuma yanã rãyar da mãtan. Lalle shĩ ya kasance daga mãsu ɓarna.
- 5. Kuma Munã nufin Mu yi falala ga waɗanda aka raunanar a cikin ƙasar, kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magãda.
- 6. Kuma Mu tabbatar da su a cikin ƙasar, kuma Mu nũna wa Fir`auna da Hãmãna da rundunõninsu abin da suka kasance sunã sauna daga gare su.
- 7. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga uwar Mũsa, cẽwa ki shãyar da shi, sai idan kin ji tsõro game da shi, to, ki jẽfa shi a cikin kõgi, kuma kada ki ji tsõro, kuma kada ki yi baƙin ciki. Lalle ne Mũ, Mãsu mayar da shi ne zuwa gare ki, kuma Mãsu sanya shi ne a cikin Manzanni
- 8. Sai mutãnen Fir`auna suka tsince shi, dõmin ya kasance maƙiyi da baƙin ciki a gare su. Lalle ne Fir`auna da Hãmãna da rundunõninsu, sun kasance mãsu aikin ganganci.
