logo HARUN YAHYA

Al-Fajr - ALQUR'ANI - Harun Yahya

  • 1. Inã rantsuwa da alfijiri.
  • 2. Da darũruwa gõma.
  • 3. Da (adadi na) cikã da (na) mãrã.
  • 4. Da dare idan yana shũɗewa.
  • 5. Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)?
  • 6. Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba?
  • 7. Iramawa mãsu sakon ƙĩrar jiki.
  • 8. Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya).
  • 9. Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi suka yi gidãje)?
  • 10. Da Fir`auna mai turãku.
  • 11. Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa?
  • 12. Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu.
  • 13. Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba.
  • 14. Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka.
  • 15. To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni`ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni."
  • 16. Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni."
  • 17. A`aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya!
  • 18. Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci!
  • 19. Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa.
  • 20. Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa.
  • 21. A`aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai.
  • 22. Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã`iku na jẽre, safũ- safu.
  • 23. Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi!
  • 24. Yana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!"
  • 25. To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah.
  • 26. Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurinSa.
  • 27. Yã kai rai mai natsuwa!
  • 28. Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira).
  • 29. Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyiNa (mãsu bin umurui a dũniya).
  • 30. Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira).
SHARE
Facebook
X
WhatsApp
Telegram
QR Code
QR Code