Al-Muddaththir - ALQUR'ANI - Harun Yahya
-
1. Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi.
-
2. Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi
-
3. Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi,
-
4. Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su,
-
5. Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu.
-
6. Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri
-
7. Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure
-
8. To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho.
-
9. To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya
-
10. A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne.
-
11. Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai,
-
12. Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya
-
13. Da ɗiyã halartattu,
-
14. Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa.
-
15. Sa`an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri!
-
16. Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyinMu, mai tsaurin kai.
-
17. Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa.
-
18. Lalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur`ãni)
-
19. Sabõda haka, aka la`ane shi, kamar yadda ya ƙaddara.
-
20. Sa`an nan, aka la`ane shi kamar yadda ya ƙaddara.
-
21. Sa`an nan, ya yi tunãni
-
22. Sa`an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk.
-
23. Sa`an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa,
-
24. Sai ya ce: "Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito."
-
25. "Wannan maganar mutum dai ce."
-
26. Zã Ni ƙõna shi da Saƙar.
-
27. Kuma mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽwa Saƙar!
-
28. Bã ta ragẽwa, kuma bã ta bari.
-
29. Mai nãcẽwa ga jiki ce (da (ƙũna).
-
30. A kanta akwai (matsara) gõma shã tara.
-
31. Kuma ba Mu sanya ma`abũta wutã (wãto matsaranta) ba, fãce malã`iku, kuma ba Mu sanya adadinsu (gõma sha tara) ba, fãce dõmin fitina ga waɗanda suka kãfirta domin waɗanda aka bai wa littãfi su sãmi yaƙĩni kuma waɗanda suka yi ĩmãni su ƙãra ĩmãni, kuma waɗanda aka bai wa littãfi da mũminai bã zã su yi shakka ba, kuma domin wa ɗanda a cikin zukatansu akwai wata cuta da kãfirai su ce: "Mẽ Allah Yake nufi da wannan, ya kasance misãli?" Haka dai Allah ke ɓatar da wanda Ya so, kuma Ya shiryar da wanda ya so. Kuma bãbu wanda ya san mayãƙan Ubangijinka fãce Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba fãce wata tunãtarwa ce ga mutum.
-
32. A`aha! Ina rantsuwa da watã.
-
33. Da dare a lõkacin da ya jũyar da baya.
-
34. Da sãfiya idan ta wãye.
-
35. Ita (wutar) ɗayan manyan masĩfũ? ce.
-
36. Mai gargaɗĩ ce ga mutum.
-
37. Ga wanda ya so, daga cikinku, ya gabãta ko ya jinkirta.
-
38. Kõwane rai ga abin da ya aikata jingina ce.
-
39. Fãce mutãnen dãma.
-
40. A cikin Aljanna suna tambayar jũna.
-
41. Game da mãsu laifi.
-
42. (Su ce musu) "Me ya shigar da ku a cikin Saƙar?"
-
43. Suka ce: "Ba mu kasance munã a cikin mãsu salla ba."
-
44. "Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalautã ba."
-
45. "Kuma mun kasance muna kũtsãwa tãre da mãsu kũtsãwa."
-
46. "Mun kasance munã ƙaryata rãnar sãkamako."
-
47. "Har gaskiya (wãto mutuwa) ta zo mana."
-
48. Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba.
-
49. Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa`azin gaskiya.
-
50. Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne.
-
51. Sun gudu daga zãki.
-
52. A`aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa
-
53. A`aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira.
-
54. A`aha! Lalle ne, shi (Alƙur`ãni) tunãtarwa ce.
-
55. Dõmin wanda ya so, ya tuna.
-
56. Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara.
SHARE
1
Al-Fatihah
2
Al Baqara
3
Ali `Imran
4
An-Nisa
5
Al-Ma`idah
6
Al-An`am
7
Al-A`raf
8
Al-Anfal
9
At-Tawbah
10
Yunus
11
Hud
12
Yusuf
13
Ar-Ra`d
14
Ibrahim
15
Al-Hijr
16
An-Nahl
17
Al-Isra
18
Al-Kahf
19
Maryam
20
Taha
21
Al-Anbya
22
Al-Haj
23
Al-Mu`minun
24
An-Nur
25
Al-Furqan
26
Ash-Shu`ara
27
An-Naml
28
Al-Qasas
29
Al-`Ankabut
30
Ar-Rum
31
Luqman
32
As-Sajdah
33
Al-Ahzab
34
Saba
35
Faatir
36
Ya-Sin
37
As-Saffat
38
Sad
39
Az-Zumar
40
Ghafir
41
Fussilat
42
sh-Shuraa
43
Az-Zukhruf
44
Ad-Dukhan
45
Al-Jathiyah
46
Al-Ahqaf
47
Muhammad
48
Al-Fath
49
Al-Hujurat
50
Qaf
51
Adh-Dhariyat
52
At-Tur
53
An-Najm
54
Al-Qamar
55
Ar-Rahman
56
Al-Waqi`ah
57
Al-Hadid
58
Al-Mujadila
59
Al-Hashr
60
Al-Mumtahanah
61
As-Saf
62
Al-Jumu`ah
63
Al-Munafiqun
64
At-Taghabun
65
At-Talaq
66
At-Tahrim
67
Al-Mulk
68
Al-Qalam
69
Al-Haqqah
70
Al-Ma`arij
71
Nuh
72
Al-Jinn
73
Al-Muzzammil
74
Al-Muddaththir
75
Al-Qiyamah
76
Al-Insan
77
Al-Mursalat
78
An-Naba
79
An-Nazi`at
80
Abasa
81
At-Takwir
82
Al-Infitar
83
Al-Mutaffifin
84
Al-Inshiqaq
85
Al-Buruj
86
At-Tariq
87
Al-A`la
88
Al-Ghashiyah
89
Al-Fajr
90
Al-Balad
91
Ash-Shams
92
Al-Layl
93
Ad-Duhaa
94
Ash-Sharh
95
At-Tin
96
Al-`Alaq
97
Al-Qadr
98
Al-Bayyinah
99
Az-Zalzalah
100
Al-`Adiyat
101
Al-Qari`ah
102
At-Takathur
103
Al-`Asr
104
Al-Humazah
105
Al-Fil
106
Quraysh
107
Al-Ma`un
108
Al-Kawthar
109
Al-Kafirun
110
An-Nasr
111
Al-Masad
112
Al-Ikhlas
113
Al-Falaq
114
An-Nas